Jami’an ‘yan sanda 25 ne da wadansu sanye da fararen kaya suka kai farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Gombe a yammacin Alhamis dinnan.
Hukumar EFCC ta sanar da cewa ba ita bace ta aika da jami’an ta gidan Goje, Umarni ne daga sifeton rundunar ‘yan sandan kasa Idris Ibrahim ga jami’an sa da su je gidan domin gudanar da bincike.
Bayanan da aka samu akan wannan samame da aka kai gidan Goje yana da nasaba ne da bayanai da aka samu cewa akwai wasu miliyoyin kudade da aka boye a gidan na sa.