Munanan Illolin da ke tattare da tsaka

2

Mutane da yawa basu damu da su kau da tsaka a gidajen su ba saboda basu dauke ta wata abar da zata ta ta da hankalin masu gida ba.

Ga wasu daga cikin illolinta masu ban tsoro

1 – Idan aka bar gari a bude takan shiga tayi birgima a cikin garin , bayan an tuka wannan garinakan kamu da cutar baras wato kuturta ko wasu mugayen kuraje

2 – Idan aka bar ruwan sha a bude sai tayi amai a cikin ruwan, yawanci sai kaga an kamu da shanyewar jiki ko kuma lalacewar sassan jiki.

3 – Idan mutum ya kwanta barci bai yi addu’a ba takanyi busa a cikin idon mutum sai kaga ya wanci an samu lalacewar gani mai kyau ko a makance.

Kwanan baya an samu labarin wata mata da ta dafa shayi da tsaka a cikin butar shayina sandiyyar wannan tsaka da mijinta da yayanta duk suka bakunci lahira.

4 – Idan tsaka ta rika a gida tana iya haddasa gobara, misalign ire-iren gobara da take faruwa a yanzu. Sau da dama tsaka ce amma bamu sani ba domin ita tsak tana tare da mugayen Aljanu.

Mu kula da wannan dabba tsaka wanda take mu’amala a cikin gidajen mu, mu kula da abincin mu da abin shan mudomin mu kaurace ma wannan illa na wannan dabba. Da zaran an ganta a cikin gida ayi kokarin kasheta kuma a ambaci sunan Allahdomin tana tare da shaidanu, tana iya cutar da mutane. Ayi amfani da tsintsita ko takalmi wajen kasheta ko kuma a saka mata maganin kashe kwari.

Share.

game da Author