Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da sakataren gwamnatin Tarayya David Lawal Babachir da shugaban hukumar NIA, Ayo Oke.
Buhari ya ce Babachir ya sauka daga kujeran sa sannan a gudanar da bincike akan badakalar kwangilar cire ciyawa da ake zargin sa da hannu dumu-dumu a ciki.
Bayan haka kuma shima shugaban hukumar binciken asiri na NIA Ayodele Oke shi ma an dakatar dashi saboda bincike da za’a gudanar akan hukumar da ya shafi kudaden da aka kama a makon da ya gabata make a wani gida a jihar Legas.
Buhari ya nada Atoni Janar na kasa Abubakar Malami, Mai ba shugaban Kasa shawara akan harkar tsaro da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda zai shugabanci kwamitin da su gudanar da bincike akan su kuma su mika masa bayanan bincikensu nan da kwanaki 14.
Discussion about this post