ILIMIN JIMA’I: Ko ka san cewa mafi yawa-yawan ‘yan mata kan dauki ciki ba tare da sun shirya ba saboda rashin sani?

2

A zamanin da, karantarwa da al’adun mafi yawan kasashen Afirika bai ba da daman da na miji ya kusanci ‘ya mace ba har sai sun yi aure.

A ganinsu a wancan lokacin tabbatar da yin hakan shine zai kare mutuncin su musamman na ‘ya’ya mata a idon duniya.
Hukumar kula da bincike kan kiwon lafiya NDHS ta fitar da wasu bayanai a shekarar 2013 inda suka nuna cewa a kasa Najeriya kashi 23 bisa 100 na ‘yan matan da ke tsakanin shekaru 15 zuwa 19 na dauke da ciki ko kuma sun riga sun taba haihuwa.

A bayanan da hukumar ta bayar ya nuna cewa matan da suke zama a karkara sun fi saurin dauka ciki kan wadanda suke zaune a birane sabo da waye wa da ilimin da suke samu a makarantun da suke zuwa a can.

Yankin Arewa maso Yamma ne ya fi yawan irin wadannan yaran da suke fadawa cikin matsaloli irin haka domin yankin kawai na da kashi 36 bisa 100 na yawan irin wadannan ‘yan mata a kasa ba ki daya.

Yankunan kudu maso Yamma da kudu maso Gabas suna da kasha 8 bisa 100.

Ilimantar da yara musamman ‘yan mata akan jima’I da kuma dabarun da za su bi domin samun kariya daga kamuwa da wasu cututtuka da daukan ciki ba’a shiyra ba na da mahimmanci saboda hakan ne kadai zai iya rage yaduwar cuta da shigan cikin da ba a shiri masa ba.

PREMIUM TIMES ta yi hira da wasu ‘yan mata kuma kusan duk bayanan da suka bada ya karkata ne zuwa ga rashin sani.

Rakiya Rabilu mazauniyar karamar hukumar Bwari, ta ce ba ta da wata masaniya akan saduwa da namiji ko alokacin da ta sadu da da namiji na farko.

Rakiya ‘yar shekara 17 ne kuma ta na sana’ar saida soyayyar gyada ne.

Ta ce ta fara saduwa da da namiji na farko ne a rayuwarta a lokacin da ta ke shekara 15 tare da wani saurayin ta mai suna Shittu wanda ke sana’ar siyar da ruwa a amalanke.

Sun dan fara soyayya ba da dadewa ba sai suka fara kusantar juna ta hanyar jima’a. Nan da nan ko sai ciki ya shiga.

Rakiya ta ce goggonta ce ta fara ganewa tana dauke da ciki a wannan lokacin sai ta shawarce ta da ta sanarwa Shittu domin ya aure ta amma ko da ta fada masa sai yaki amincewa ya ce ba zai aure ta ba sai bayan ta haihu.

A yanzu haka Rakiya ta ce Shittu mahaifin danta ya gudu kuma babu wanda ya san inda yake.

Rakiya ta koka da matsalar karancin sani akan ilimin jima’a a matsayin dalilan da ya sa hakan ya faru da ita tun farko da hakan bai faru ba.

Ita kuma Roselyn Joseph ‘yar shekara 16 ta ce tabas tana da masaniya akan harkan yin jima’I kuma ta san yadda za ta kare kanta daga daukan ciki da kuma wasu cuttuttuka domin saurayin ta da take saduwa da shi yana amfani da kwaroro roba.

Ta ce ta sami wannnan ilimin ne daga wajen wata malamar su da take koyar dasu darasi akan jima’ai da kuma yadda za a sami kariya daga daukan cuttutuka musamman cutar kanjamau.

Roselyn ta koka da yadda ta fara yin juma’I da wuri saboda duk sauran kawayen ta ba su riga sun fara ba duk da cewa ta san yadda za ta sami kariya daga daukan ciki da kuma cuttuttuka.

Bolutife, Grace Onwukwe mai shekar 15 ta ce ta san me ake mufi da juma’I kuma da irin cututtukan da za a iya dauka ta dalilin hakan domin an koya mata a makaranta.

Ta ce ta amince da ta hakura har sai bayan ta yi aure saboda tana tsoran daukan ciki da wuri.

Wata babban jami’a a hukumar NACA Hafsatu Aboki ta ce hukumar wanda nauyin ilmantar da ‘yan Najeriya akan jima’i ya rataya a kai na iya kokarin ta wajen ganin cewa matasa musamman mata sun gane matsalolin da za a iya fuskanta idan har ba a sami cikaken bayanai akan saduwa da da namiji ba kafin a afka wa abin.

Hafsatu ta ce hukumar su ta fara yin hakan ne a shekarar bara inda ta fito da wasu shirye-shirye da ake kira ‘’National HIV Strategy for adolescent and young people’’ domin wayar da kan mutane musamman matasa wadanda ke birane da kauyuka akan mahimmancin rashin fara yin jima’I da wuri, kaurancewa yin jima’I har sai bayan anyi aure da kuma dabarun da za a iya bi idan har ta kama dole mutum sai yayi domin samun kariya daga cututtuka musamman kanjamau.

Share.

game da Author