Sanata mai wakiltan Barno ta kudu ya samu kasaitacciyar tarba daga mutanen yankin Barno ta Kudu da yake wakilta.
Majalisar Dattijai ta dakatar da Ali Ndume har na tsawon kwanaki 181 saboda wai ka ma shi da tayi yana bada bayanan karya akan wasu ‘ya’yan majalisar da ya hada da shugaban majalisar, Bukola Saraki.
A taron Ali Ndume ya shaida wa dandazun magoya bayan sa a jihar cewa ba zai roki shugaban majalisar ba ko wai don a dawo dashi saboda a iya sanin sa bai aikata wani laifin da zai sa a dakatar dashi ba.
“Ina so in sanar mu ku cewa na yi matukar farin cikin wannan tarba da akayi mini. Duk da cewa an nemi da in rubuta wasika ga shugaban majalisar akan ya hakura a dawo dani majalisar, na ki yin haka saboda ni har yanzu ban ga laifin da nayi ba da za’a ce wai in je in roki wani. An nemi da in sasanta da su na ce babu abin da zan sasanta akai saboda ban aikata laifi ga kowa ba.
Ndume ya shaida wa magoya bayansa ainihin dalilan da ya sa aka dakatar dashi a majalisar.
“Na fara samun matsalane tun bayan nuna goyon bayana ga kudirorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake aiko wa majalisa. Sannan Kuma da kokarin ganin cewa majalisar ta amince da nadin Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC. Na tsaya tsayin daka a matsayina na shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai. Hakan bai yi ma wasu dadi ba.
“Shugaban Majalisar yana da ikon ya dakatar da ni a lokacin da na tashi a majalisar domin gabatar da korafi na, amma da yak e suna da wata shiri da ba ni da masaniya akai sai ya bari domin suci mutunci na.
Sarakunan Biu da Shani sun tabbatar wa Sanata Ali Ndude goyon bayansu dari bisa dari sannna sun jinjina masa akan kyawawan ayyukan da yake yi wa mazabunsa.