Tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya jinjina wa yaki da cin hanci da rasahawa da gwamnantin Buhari ta keyi a kasa yanzu.
Shekarau ya fadi hakanne da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarai a garin Sokoto ranar litini.
“ Duk wanda ya wawuri kudin da ba na sa ba dole ne a bincike shi sannan a hukunta shi.
“ Babu wani wanda ya fi karfin hukuma saboda haka dole ne kowa ya bi doka.
Yayi kira ga gwamnati da kara yawan kudaden da ta ke ba fannin tsaro a kasa.
Shekarau yaba da tabbacin cewa jam’iyyar PDP zata karbi mulki a 2019.