Sarkin Musulmi zai jagoranci addu’o’I na musamman domin nema ma shugaban kasa Muhammadu Buhari Karin lafiya da kuma samun zaman lafiya mai dorewa a kudancin jihar Kaduna.
Sakataren kungiyar Jama’atu Dr. Khalid yace za’a gudanar da zaman addu’o’in ranar Lahadi mai zuwa a garin Kaduna.
Yace gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai, Sarkin Zazzau, Shehu Idris, Sarkin Musulmi, Dr, Abubakar Sa’ad da Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna duk za su halarci zaman addu’o’in.
Bayan haka sarkin musulmi Abubakar Sa’ad yace masallatan Juma’a a jihar su gudanar da irin wadannan addu’o’I a masallatansu ranar juma’a.
A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu ya jagoranci malamai da limaman jihar domin gudanar da addu’a ta musamman na neman Allah ya karawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari lafiya.
An gudanar da taron addu’an ne a babban filin idi da ke jihar.
Bayan haka kuma an yi irin hakan a garin Bauchi inda gwamnan jihar Mohammed Abubakar da sarkin Bauchi Rilwanu Adamu suka jagoranci addu’o’in.
A lokacin gudanar da wannan addu’o’i sarkin Bauchi yayi kira ga masarautun dake kasar Bauchi duka da su gudanar da irin wadannan addu’o’i ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya na kasar Ingila inda yake hutu da ganin likitoci kan lafiyarsa.
Yayi Magana da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje a makon da ya gabata a daidai ana gudanar da addu’o’i domin samun lafiyarsa a fidar gwamnatin jihar.
Buhari ya godewa ‘yan Najeriya da irin nuna damuwarsu akan lafiyarsa da sukeyi sannan ya ce yana samun karin lafiya akullum wayewar gari.