Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta sha kyar a hannu kungiyar kafa ta Las Palmas inda ta buga 3 da 3 a wasan kwallon kafa na Laliga da aka buga yau a filinta na BernaBau.
Madrid ne ta fara jafa kwallo a ragar Las Palmas in da daga baya Las palmas suka surfafesu kamar ba gobe suka jefa musu kwallaye 3 bayan haka.
Cikin minti goma kafin karshen wasan Madrid ta farke kwallaye biyu ta hannun shahararren dan wasanta Ronaldo in da wasan yak are 3 da 3.
Har yanzu dai Kungiya kwallon kafa ta Barcelona ne take sama da Madrid da maki 57 in da ita kuma Madrid take da maki 56 amma da kwantan wasa daya a hannun ta.
Yau Barcelona ta lallasa Sporting da ci 6 da 1.