Gwamna Kashim Shettima ne ya cancanci ya gaji Buhari – Dan Majalisa

0

Wani dan majalisar dokokin jihar Barno, Danlami Kubo yace babu wanda ya cancanci zama shugaban kasa bayan Buhari ya kammala lokacinsa kamar gwamnar jihar Barno, Kashim Shettima.

Dan majalisar yace suna nan sun fara shiri domin ganin wannan buri nasu ya tabbata.

Ko da yake gwamna Kashim shettima bai nuna cewa ya na da niyyar neman shugabancin kasa Najeriya ba bayan wa’adin mulkin Buhari ya cika, dan majalisa Danlami yace sun fara shirin hakan.

Danlami yace da gaske suke yi akan wannan yaki da suka sa a gaba kuma za su ci gaba da neman hakan har sai burinsu ta cika.

Da yake yabon gwamna shettima, Danlami yace irin shugabancin da gwamnan ya keyi a kungiyar gwamnonin Arewa ya nuna cewa zai iya zama magajin Buhari.

Kuma hakan ya nuna cewa koda kasa Najeriya ce aka bashi zai nuna bajintarsa.

“ Shettima ya hada kan musulmai da kiristocin jihar sannan ba ya nuna banbanci a tsakanin mutane.

Danlami yace zai ci gaba da bibiyan wannan manufa tasi har sai ya samu nasara akan hakan.

Yace zai yi amfani da kujeransa na dan majalisa domin kira ga abokanan aikinsa da su mara ma wannan aiki da ya sa a gaba baya.

Share.

game da Author