Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kira gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, a daidai suna yi masa addu’a a fadar gwamnatin jihar Kano.
Gwamnan Ganduje ya gaiyaci manyan malamai zuwa fadar gwamnati domin gudanar da addu’a ta musamman ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Adaidai suna gab da fara karatun Al’kur’ani Kenan sai Buhari ya kira gwamnan inda shi Ganduje ya saka shugaban kasa Muhammadu Buhari a na’urar kara sauti wato (Loud speaker) domin kowa yaji abinda zai ce.
Buhari ya gode wa malaman da gwamna Ganduje sannan yace yana samun Karin sauki a duk wayewan gari.
Malamai da wadansu yan Najeriya ne suka halarci taron yin addu’ar a fadar gwanmantin jihar Kano.