Nuhu Abdullahi jarumi ne wanda yayi fice a shirya Fina-finan Hausa a arewacin Najeriya.
Nan da dan wasu kwanaki, wannan matashin jarumi zai kaddamar da wata sabuwar fim dinsa mai suna ‘Gudun Tsira’ ga masoyansa, jarumai da manema labarai a garin Kano.
Kamar yadda ya shirya kaddamar da wannan fim nasa, Nuhu ya na so yayi abun da ba’ataba yi ba a farfajiyar Fina-finai Hausa, inda a karo na farko zai hada duka wanda zasu fito a fim din da wadanda zasu yi wata hidima a wajen shirya fim din ga maneman labarai domin su tattauna akan yadda za su tunkari shirya fim din.
Bayan haka jaruman da zasu fito a fim din zasu halarci bukin kaddamar da fara shirya fim din sannan za su tattauna da juna da wasu kwararru da za’a gaiyata.
Jarumai kamarsu Hadiza Gabon, Jamila Nagudu, Fati Washa, Ali Nuhu, Falalu Dorayi da dai sauransu ne zasu fito a ‘Gudun Tsira’ kuma duk zasu halarci bukin kaddamarwan.
“ Kamar yadda kowa ya sani cewa irin haka shine na farko da za a yi a farfajiyar finafinan Hausa, nayi hakanne domin kara daukaka shirye-shiryen finafinan mu da ganin ta yi daidai da yadda ake yi a kasashen da suka ci gaba.” Inji Nuhu Abdullahi.
Za’ayi bukin ne ranar 28 ga watan Faburairu.