Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya godewa ƴan Najeriya bisa goyon bayan da suka bashi tun daga lokacin da ya fara mulkin sa a 2015 zuwa yanzu da wa’adin mulki ya zo karshe.
A jawabin bankwana da yayi, shugaba Buhari ya roki ƴan Najeriya su yafe masa a inda ya gaza a tsawon mulkin sa.
” Ku ya fe min domin na san wasu daga cikin manufofin da kirkiro kuma muka zartas da kyawawan niyya sun jefa wasu cikin mawuyacin hali da tsananin rayuwa, ina rokon ku ƴan Najey ku yafe min
” Na yi yaki da cin hanci da rashawa a lokacin mulkina ka-in da na-in, kamar babu gobe, kuma mun samu nasarar gaske
” Kuma Har yanzu ina bakin ciki da jimamin ƴan matan Chibok da sauran waɗanda aka sace a faɗin kasar. Abin yana min ciwo matuka.
A cikin jawabin sa na bankwana shugaba Buhari ya bayyana cewa a iya tsawon mulkin sa, ya gyara Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015.
Discussion about this post