Gwamnan Kano mai barin gado Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa zai mika mulki ga sabon gwamna Abba Yusuf ranar Lahadi saboda ba aya so ya kuskure rantsar da shugaban kasa Bola Tinubu a Abuja.
Kwamishinan yada labarai mai barin gado na jihar, Mohammed Garba ne ya fitar da haka a takarda daga fadar gwamnatin Kano.
Garba ya ce Ganduje tare da kwamitin shirya mika ga sabuwar gwamnati na bangarorin biyu duka sun haɗu kuma sun gama komai.
” Ranar Lahadi Ganduje zai mika mulki ga Abba, daga nan sai ya tashi zuwa Abuja domin ci gaba da shirye-shirye da kuma halartar rantsar da shugaban Kasa Bola Tinubu.
Discussion about this post