Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabiu Kwankwaso zai gana da gwamnan jihar Ribas Nysome Wike a garin Fatakwal.
Wannan ganawa na da alaƙa da takarar Kwankwaso shugaban Kasa kamar yadda bayanai suka ka iske mu.
Majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa gwaskayen biyu za su gana kuma akwai yiwuwar maganar wanda zai yi wa Kwankwaso takarar mataimakin shugaban kasa ne ke kan gaba a tattaunawar.
Kwankwaso da Wike na da kyakkyawar alaka a tsakanin su wanda masu yin sharhi suka ce yayi wa Wike tasiri a zaɓen fidda gwani na PDP wanda Atiku yayi nasara.
Sai dai kuma Wike ya taɓa cewa ba zai taɓa ficewa da ga APC ba ko bayan da aka suntuma shi da kasa a zaben fidda gwani.
An yi zaton Wike ne Atiku zai zaɓa mataimakin sa amma kuma sai ya zaɓi gwamnan jihar Delta Okowa a matsayi wanda za su yi takara tare.
Tun daga wannan lokacin Wike bai ƙara cewa komai ba sannan kuma bai fito ya taya Okowa murnar zaɓen sa ɗan takarar mataimakin shugaban kasa.
Haka kuma wasu ƴan majalisar dokokin jihar Ekiti da ke tare da tsohon gwamnan jihar Ayo Fayose,sun bayyana goyon bayan su ga Wike.
A wata wasika da suka aika wa Wike sun ce duk inda ya tafi za su ba shi kariya dan hakan ma ya tabbata.
” Muna tare da kai Wike. Ba za mu taba yi maka butulci ba saboda irin goyon baya da bauta da ka yi wa jam’iyyar PDP.
Discussion about this post