Ɗan majalisan dake wakiltar birnin Kano a majalisar Tarayya, Sha’aban Sharada ya garzaya kotu yana ƙalubalantar zaɓen mataimakin gwamnan Kano Nasir Gawuna ɗan takarar gwamnan jihar na Jam’iyyar APC.
Sharaɗa ya bayyana a kotu cewa an karya dokar zaɓe ta hanyar saka Daliget ɗin da doka bata basu damar jefa kuri’a ba su jefa a lokacin zaben ɗan takarar gwamnan jihar Kano.
A dalilin haka, Sharaɗa ya ce a soke wannan zaɓe domin ba a bi ka’ida ba kamar yadda dokar zaɓe ta gindaya.
Babban kotun tarayya inda a nan ne aka shigar da kara ta ce za ta saurari wannan ƙara bayan an aika wa mataimakin gwamna Gawuna takardar sammaci.
Sai dai kuma Lauyan Sharaɗa ya shaida cewa kotu cewa ko da aika wa Gawuna takardar sammaci ya ki amsa da gangar.
Alkalin kotun M Liman ya ce ya rage ranar da za a fara sauraren karar daga kwanaki 30 daga ranar zuwa kwanki 15 masu zuwa.
Idan ba a manta ba, Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya mara wa mataimakun sa Nasir Gawuna baya don ya gaje shi idan Wa’adin sa ya cika.
Sule Garo wanda aka fi sani da Kwamanda shine jam’iyyar APC ta yadda ya yi takarar mataimakin gwamna.
Zaɓen jihar Kano a 2023 zabe ne wanda mutane da dama suka saka ido suna jiran suga yadda za ta kaya.
Babbar kalubalen dake gaban APC ita ce yadda za ta kayar da jam’iyyar NNPP, jam’iyyar Kwankwaso.
Discussion about this post