Babbar Kotun Tarayya ta hamɓarar da ƙarar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Ministan Shari’a Abubakar Malami su ka shigar, wadda wadda su ka ƙalubalanci Sashe na 84(14) na Sabuwar Dokar Zaɓe.
Manyan Alƙalai bakwai ne su ka zartas da hukuncin, bisa shugabancin Mai Shari’a Musa Dattijo-Muhammad, gaba ɗayan su sun amince da korar ƙarar, sun kuma kira ƙarar cewa Buhari da Malami na ƙoƙarin yi wa kotu karan-tsaye.
Mai Shari’a Aokmaye Agim ne karanta sakamakon hukuncin, inda ya bayyana cewa “tunda dai har Buhari ya saka wa Sabuwar Dokar Zaɓe ta 84(12) ta 2022 hannu, to ba shi da wani dalili ko hujjar da zai garzaya kotu ya nemi a soke dokar, bayan ya saka mata hannu.
“Babu wani wuri a cikin Kundin Dokokin Najeriya inda doka ta ba Shugaban Ƙasa ikon ya nemi kotu ta sake wata doka, bayan ya rigaya ya sa mata hannu. Haka kuma babu dokar da ta ba Shugaban Ƙasa ikon ya nemi kotu ta maido wata dokar da shi shugaban ya ƙi sa mata hannu, bayan wa’adin sa mata hannun ya wuce.” Inji Mai Shari’a Agim.
Kotu Ƙoli ta ci gaba da cewa hatta roƙon da Shugaba Buhari ya yi wa Majalisa a Najeriya, inda ya nemi su goge dokar bayan ya rigaya ya sa mata, shi ma haramtacce ne, kuma ya karya doka.
Agim ya ce Buhari da Malami sun shigar da ƙara don kawai a tunanin su kotu za ta amince da soke wata dokar da Buhari ya yi.
Wannan kuwa inji shi ba abin saurare ha ne a kotu, bisa la’akari da Sashe na 1(1) (a) na Ƙarin Ƙarfin Ikon Kotun Ƙoli.”
Sauran mambobin Alƙalan da su ka fatattaki Buhari da Malami daga kotu, sun haɗa da Dattijo Muhammad, John Okoro, Amina Augie, Lawal Garba da Ibrahim Saulawa.
Dajin Da Aka Keto Kafin Kotun Ƙoli Ta Kori Ƙarar Da Buhari Da Malami Su Ka Shigar:
Idan ba a manta ba, Buhari da Minista Malami sun maka Majalisar Tarayya Kotun Ƙoli saboda fatawar Sashen 84(12) na Sabuwar Dokar Zaɓe.
Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Shari’a Abubakar Malami, sun garzaya Kotun Ƙoli, su na neman a yi masu fassara da sharhin ma’anar wani sashe na Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022.
Buhari da Malami sun shigar da ƙarar tun a ranar 29 Ga Afrilu, inda su ka maka Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya kotu.
Sashe na 84(12) na Sabuwar Dokar Zaɓe dai ya shiga harankazamar ja-in-ja a Najeriya, tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022 hannu cikin watan Fabrairu.
Jim kaɗan bayan Buhari ya sa wa ƙudirin dokar hannu ta zama doka, ya roƙi Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa cewa su soke wancan sashe da ake ta tankiya a kan sa, amma su ka yi ƙememe, su ka ƙi goge shi.
Abin Da Sashe Na 84(12) Ya Ƙunsa:
“An haramta wa mai riƙe da muƙamin siyasa ko muƙamin gwamnati ko shugabancin jam’iyya yin zaɓe a matsayin wakilin masu zaɓen ‘yan takara. Kuma ba a yarda a zaɓe shi ba, sai da idan ya ajiye muƙamin sa.”
Idan ba a manta ba, watanni biyu da su ka gabata, Babbar Kotun Tarayya ta Umuahia a Jihar Abiya ta soke wannan sashe na 84(12), bisa dalilin cewa ya ci karo da Kundin Dokokin Najeriya.
Shawagin-ɓiɗar-kaɗen Minista Malami:
Minista Malami ya yi azarɓaɓin cewa zai soke dokar domin bin umarnin Babbar Kotun Tarayya ta Umuahia. Sai dai kuma a lokacin ya na da kwaɗayin takarar gwamna a jihar Kebbi.
Kafin Malami ya soke dokar, sai Kotun Ƙoli ta yi gaggawar soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Umuahia ta zartas. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce kada a sake a soke dokar.
Ganin haka ne a yanzu Buhari da Malami su ka dira Kotun Ƙoli, domin a san matsayar wannan Sashe na 84(12) da ke cikin Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2023.
A makon jiya ne Premium Times ta buga labarin yadda Majalisar Tarayya Ta Bi Ra’ayin Majalisar Dattawa, Su Ka Yi Wa Sashe Na 84 (8) Na Sabuwar Dokar Zaɓe Kwaskwarima:
Majalisar Tarayya ta amince tare da aikawa da kwaskwarimar da su ka yi wa Sabuwar Dokar Zaɓe Sashe na 84 (8) na 2022, ta yadda wakilan zaɓen ‘yan takara masu riƙe da muƙaman gwamnati za su samu damar yin zaɓen fidda-gwani, taron gangami da tarukan jam’iyya.
Majalisar Tarayya ta yi wa sabuwar dokar kwaskwarima ce bayan ta yi la’akari da Kudirin da Shugaban Kwamitin Majalisa Abubakar Fulata ya gabatar a ranar Laraba, a Abuja.
Kudirin dai mai suna, “Kudirin Yin Kwaskwarima Ga Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022 Mai Lamba 13”, ya bayar da dama ga wakilan jam’iyya masu riƙe da muƙaman gwamnati su yi zaɓe a lokacin zaɓukan fidda-gwanin ‘yan takarar jam’iyyu.
Idan an tuna, Sabuwar Dokar Zaɓe wadda Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa hannu cikin watan Fabrairu 2022, ta haramta wa masu riƙe da muƙaman gwamnati su yi zaɓen fidda gwani.
Su Wane Ne Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa?:
Sun haɗa da: Kansilolin mazaɓu da ke ƙananan hukumomi, shugabannin ƙananan hukumomi da mataimakan su, shugabannin jam’iyyu na ƙananan hukumomi 774, ‘yan majalisar dokokin jihohi da ‘yan majalisar tarayya.
Sauran sun haɗa da: Gwamnoni, mataimakan gwamnoni, shugaban ƙasa da mataimakin sa, Shugabannin Majalisar Gudanarwar Jam’iyya, shugabannin jam’iyya na jihohi, na ƙananan hukumomi da sakatarorin su.
Wannan sabuwar doka da aka yi wa kwaskwarima za ta bai wa waɗannan da aka lissafa a sama su yi zaɓen ‘yan takara a zaɓen fidda gwani.
Idan ba a manta ba, Majalisar Dattawa ta amince da wannan kwaskwarima tun a ranar 10 ga Mayu, 2022.
A farkon shekarar nan PREMIUM TIMES Hausa ta riƙa kawo kwatagwangwamar da ta dabaibaye wannan sabuwar doka. Har ta kai an bada wani rahoton da babban lauya Femi Falana ya zargi Ministan Shari’a Abubakar Malami da yin surunkutumi cikin sha’anin hukuncin kotu.
‘Yadda Ministan Shari’a Malami ya damalmala hukuncin kotu a kan Dokar Zaɓe’ -Femi Falana:
Babban Lauya mai rajin kare haƙƙi da ‘yancin jama’a Femi Falana ya zargi Ministan Shari’a Abubakar Malami da damalmala Babbar Kotun Tarayya ta yadda ta bayar da hukunci baddalalle mai cike da tarnaƙi akan matsayar sashe na 84(12) na Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022.
Falana ya ce Malami ya yi bakam, ya nuna kamar bai ma san akwai wani hukunci ko umarnin kotu wanda na Kotun Tarayya wanda ya haramta masa yin katsalandan a kan dokar. Amma sai ya jajirce cewa shi sai ya yi amfani da umarnin Babbar Kotun Umuahia, wadda ta bayar da umarnin a soke wannan sashen ɗungurugum.
Falana wanda babban lauya ne (SAN), ya fitar da sanarwa inda ya bayar da cikakken bayanin yadda Manyan Kotunan Tarayya guda uku suka bayar da mabanbantan hukunce-hukunce. Daga nan Falana ya ɗora laifin gaba ɗaya a kan Ministan Shari’a Malami.
“Don haka sai Falana ya ce ya kamata Malami ya sani cewa ba fa zai iya yin yadda ya ga dama ba, ta hanyar bin umarnin da ya ga dama, kuma ya bijire wa wadda ya gada dama.
“Sannan kuma babu sauran wata jikara ko tantama, tabbas Ministan Shari’a ya damalmala hukuncin Babbar Kotun Tarayya har ta bayar da baddalallun hukunce-hukunce a kan sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe ta 2022.” Inji Falana.
Discussion about this post