Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya tabbatar wa al’ummar Kaduna cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tukuru don ganin jihar Kaduna ta ƙasaitacciyar jiha a faɗin Najeriya.
Yayin da yake taya al’ummar jihar murnar bikin Sallah a Kaduna a ranar Laraba, gwamnan ya ce gwamnatinsa na samun ci gaba a kai a kai kuma ya kuduri aniyar maida Kaduna abin alfaharin ga duk wani ɗan jihar da ma baƙi.
Ya kuma ce gwamnatinsa za ta mai da hankali matuka wajen bunkasa yankunan karkara ta hanyar samar musu da ababen more rayuwa.
“Muna so mutanen karkara su shaida cewa lallai akwai gwamnati da ta damu da jin daɗin su sannan kuma gwamnati na ta mayar da hankali ne wajen ganin jihar Kaduna ta zama cibiyar kasuwanci da masu sakanjari a duk faɗin duniya za su rika rigerigen zuwa don saka jarinsa a jihar.
Haka kuma, gwamna Sani ya jaddada bukatar hada karfi da karfe domin magance matsalar ‘yan fashi da ta’addanci a jihar da Najeriya baki ɗaya.
” A Jihar Kaduna, ba mu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin mun yi maganin masu aikata miyagun laifuka da ke yiwa al’ummarmu kawanya. Mun kulla kwakkwarar hadin gwiwa da jami’an tsaro na tarayya tare da karfafa hukumar ‘yan banga ta Kaduna (KADVS).
“Mun dauki matakai don inganta hanyoyin tara kudaden shiga da ake samu a cikin jihar, da rage tsadar gudanar da mulki.
A ƙarshe gwamna Uba ya mika sakon taya murna ga ɗaukacin musulmai game da kammala azumin Ramadana da kyma na bukukuwan sallah da aka yi.
Discussion about this post