Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin Kare Haƙƙi na Najeriya, Reshen Jihar Taraba, Joseph Gimba, ya bayyana ɓacin rai da yin Allah-wadai da irin gagarimar tarbar da mutanen garin Ibbi a cikin jihar, suka yi wa gogarma Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume.
Hamisu Wadume ya dira garin su Ibbi bayan kammala wa’adin ɗaurin shekaru bakwai da kotu ta yi masa a gidan kurkuku Kuje, da ke FCT Abuja.
Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin CCSGN na Jihar Taraba, Hassan Gimba, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa gagarimar tarba da irin shagulgulan da aka yi a Ibbi saboda murnar kammala zaman kurkukun Wadume, abin takaici ne matuƙa, abin Allah–wadai da tir ne, kuma babban laifi ne.”
Wadume dai an ɗaure shi shekaru bakwai cikin 2019, makonni kaɗan bayan da wasu sojoji suka kai hari kan tawagar ‘yan sandan da suka kamo Wadume daga Inji, Jihar Filato, yayin da suke kan hanyar su ta kai shi Abuja.
Sojojin dai su na ƙarƙashin Bataliya ta 93, ƙarƙashin Tijjani Balarabe, sun tsaya a shingen bincike ne da ke tsakanin titin Ibbi zuwa Takum.
Sun buɗe wa ‘yan sanda wuta, suka kuɓutar da Wadume, bayan sun kashe wasu ‘yan sandan a ranar 6 ga Agusta, 2019.
A wurin dai an kashe ‘yan sanda uku da farar hula biyu, sannan wasu ‘yan sanda biyar suka ji ciwo sosai.
Daga baya an kamo Wadume a Kano, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 7 a Kurkukun Kuje, FCT Abuja, bisa laifin tserewa daga kamun da ‘yan sanda suka yi masa da kuma tu’ammali da bindigogi ba bisa ƙa’ida ba.
Masu gabatar da ƙarar Wadume sun kasa gabatar wa kotu da hujjojin cewa Wadume mai garkuwa da mutane ne.
PREMIUM TIMES ta gano cewa an sallami Wadume ranar Juma’a, bayan ya kammala zaman gidan Yari na shekaru bakwai a Kuje, bisa ɗaurin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yi masa.
Mazauna garin Ibbi sun yi masa gagarimar tarba, suka yi dafifi a ranar Lahadi.
Da ya ke bayanin abin da ya kira a matsayin abin takaici, Gimba ya ce, “abin takaici ne a wai har wasu za su fito su na shagulgulan murnar gogarman maɓarnaci ya kammala zaman kurkuku ya dawo cikin su. Alhaji kuma irin su ne ke haifar da masifu a cikin al’umma.
“Ba a samu lokacin da aka yi ƙwaƙƙwaran bincike kan zargin da aka yi masa ba, kafin kotu ta yanke masa hukunci. Shi ya sa aka ɗaure shi shekaru 7 kaɗai. To amma gaskiya bai dace a yi murnar sallamar sa daga kurkuku ba,” inji Gimba.
“Daga cikin manyan matsalolin ‘yan Najeriya akwai talauci na fatara da kuma talaucin rashin sanin abin da ya dace. Mu na bai wa dukiya daraja sosai. Mutane babu ruwan su da irin ɓarnar da ya riƙa tafkawa. Jira kawai suke yi ya koma cikin su ya ci gaba da raba masu kuɗaɗen haram.”
PREMIUM TIMES ta gano cewa yayin da ya isa gida, Wadume ya kai ziyarar gaisuwa wurin Sarkin Ibbi, Danbawuro, bayan ya yi wa dandazon mutanen da suka tarbe shi jawabin godiya.
Sarkin Ibbi Salihu Danbawuro ya ce shi da mutanen masarautar sa sun yi murna da farin cikin ganin ɗan su Wadume ya koma gida, bayan kammala zaman kurkuku.
Shi ma Wadume ya gode wa Sarki da mutanen garin, saboda goyon bayan da ya ce sun ba shi tun bayan ɗaure shi har sallamar sa.
“Ni da ɗaukacin mutanen masarauta ta nuna murna da dawowar Hamisu Wadume garin su Ibbi,” cewar basaraken Ibbi ɗin.
Discussion about this post