Babbar Kotun Kano ta tabbatar da halascin dakatarwar da Shugabannin APC na Mazaɓar Ganduje suka yi wa Shugaban APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje.
Yayin da ake yanke hukunci a ranar Laraba, Babbar Kotun Kano ta kuma gargaɗi Ganduje cewa ya daina kiran kan sa a matsayin mamba na APC, domin a yanzu shi dakatacce ne.
Mai Shari’a Usman Na’abba ne ya yanke wannan a ranar Talata, kamar yadda wani kwafen shari’ar ya nuna, wanda gidan Talabijin na AIT da kuma jaridar Daily Trust da wasu jaridu suka wallafa.
Wannan umarnin da aka ba Ganduje ya biyo bayan ƙarar da Lauyan Haladu Gwanjo da Laminu Sani, mai suna Ibrahim Sa’ad ya shigar.
Gwanjo da Sani dai Shugabannin Zartaswa ne na APC a Mazaɓar Ganduje da ke cikin Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, a Jihar Kano.
Sun ce sun shigar da ƙarar ce a madadin sauran shugabannin jam’iyyar na Mazaɓar Ganduje baki ɗaya.
Gwanjo wanda ya ce shi ne Mashawarcin APC a fannin Shari’a, shi ne kwanaki biyu da suka gabata ya bayyana sanarwar dakatar da Ganduje daga APC a Mazaɓar Ganduje.
Babbar Kotun Kano ta ce kada Ganduje ya ƙara shugabantar gudanar da duk wasu al’amurran da suka shafi APC a matakin shugabancin sa na ƙasa.
Mazaɓar Ganduje ta dakatar da shi ne bisa zarge-zargen harƙallar kuɗaɗen da gwamnatin Kano ke zargin ya tafka.
Discussion about this post