Jam’iyyar APC ta shiyyat Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Ganduje
Mai baiwa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a shiyyar, Haladu Maigwanjo ne ya sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Kano ranar Litinin.
“Mambobin sun yanke shawarar dakatar da shugaban kungiyar na kasa ne saboda kasa wanke sunansa daga zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi masa, wadanda suka hada da faifan bidiyon dala da ake yadawa inda ake zargin yana karbar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila. ” inji Maigwanjo.
Sai dai kuma jim kaɗan bayan dakatar da Gandujen, sai shugaban jam’iyyar na jihar Abdullahi Abbas ya sanar da dakatar da Maigwanjo na wata shida bisa zargin yi wa jam’iyyar APC a jihar zagon Kasa.
” Muna da hujjoji karara da ke nuna wani taron sirri da Maigwanjo ya yi da wakilan gwamnatin Kano domin a ci mutuncin Ganduje. Saboda haka mun dakatar da shi kuma ya dakatu a yanzu.
Idan dai ba a manta ba, tsohon shugaban jam’iyyar Adams Oshiohole ya rasa kujerars a ta shugabancin jam’iyyar APC be a irin haka bayan mazabar sa ta dakatar da shi
Discussion about this post