Mazauna babban birnin tarayyar Najeriya Abuja sun koka kan yadda suke fama da tsananin bala’in matsin rayuwa a wannan gari a halin yanzu.
Mazaunan sun shaida cewa baya ga tsadar rayuwa da cigaba da hauhawar farashin kayan masarufi da na yau da kullum, albashin ma’aikaci yanzu ba ya isa a ci abinci ma kawai ba tare da an yi maganar sauran ɗawainiyar Iyali ba.
Masu motocin Haya suma sun koka tsananin rashin fasinja da suke fama da sannan kuma da cewa ɗan abin da suka samu ba ya isan su iya biya wa kansu bukatu na yau da kullum.
Wani ma’aikacin gwamnati mai suna Ekaite Akpan ya bayyana cewa da yawan su sun dogara ne da motocin haya wajen zuwa aiki a kullum sai dai kuma abin yana neman ya gagara yanzu domin kuɗin mota ya yayi tsadar gaske. “Kusan albashin mutum kaf a motar haya ya ke karewa”.
Ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta shigo da motocin da ta yi alkawarin kawowa domin ma’aikata su samu sauki.
Bincike ya nuna cewa daidai da ruwan leda da ake saida naira 20 a wasu jihohin, a Abuja naira 50 ya ke. Haka kuma ba a maganan burodi da sauran kayan masarufi.
Mutane sun koka matuka game da yadda jama’a ke fama da tsananin matsin rayuwa a wannan lokaci sannan kuma abu ya ki ci ya ki cinyewa har yanzu.
Wani magidanci, ya ce ” A kullum abubuwa sai kara faskara masa suke yi suna nemansu ƙarfinsa, “zaman Abuja ya na neman ya gagari ba ma talaka ba, har da mai dan karamin karfi da ma’aikatan da ba su da albashi mai kauri.
” Yau ko da albashin ka mai kauri ne, ba zai ishe ka dawainiyar kanka ba, ballantana ka hada da na Iyali.
Da yawa daga cikin mutane sun roki gwamnati ta gaggauta samar da mafita ga jama’a domin a na cikin tsananin matsin rayuwa a kasar.
Discussion about this post