Ministan Kasafin Kuɗaɗe da Tsare-tsare, Atiku Bagudu, ya bayyana cewa Dokar Najeriya ta bai wa ‘Yan Majalisa iznin yin ƙarin cushen ayyukan cikin kasafin da gwamnati ta aika masu domin su yi nazari.
Bagudu ya bayyana hakan a lokacin da ya kira taron manema labarai, dangane da ruɗanin zargin cushen biliyoyin nairori da ake zargin Majalisar Dattawa ta yi a kasafin 2024.
PREMIUM TIMES ta ruwaito zargin cushen Naira biliyan 3.7, wanda Sanata Abdul Ningi ya yi, a wata hira da Gidan Radiyo na BBC Hausa ya yi da shi.
Sai dai kuma da ya ce bayani dangane da wannan gutsiri-tsomar da ta kai ga fusata majalisa har ta dakatar da Ningi tsawon watanni uku, Bagudu ya ce ai cushe a cikin kasafin kuɗi, ba wani sabon abu ba ne, tunda dai ayyuka ne suke cusawa, kuma dama dokar ƙasa ta bayar da wannan damar.
Bagudu ya ce gwamnatin da ta gabata ta je Kotun Ƙoli, inda ta nemi ƙarin haske dangane da abin da Dokar Najeriya ta ce a kan cushen ayyuka da Majalisa ke yi, lamarin da aka sasanta a wajen kotu.
“Bayan gwamnatin da ta shuɗe ta je Kotun Ƙoli, sun sasanta kafin a yanke hukunci a wajen kotu. Kuma har yau ba a warware matsalar ba.
“Saboda haka dangane da wannan lamari, sai dai na ce babu wani hukunci daga Majalisar Ƙoli da ya rushe haka. Kuma a tsarin dimokraɗiyya, Majalisar Ƙasa I a ce ƙololuwa.
“Kai ko da sun fito da ƙudirin da suka aika wa Shugaban Ƙasa, amma ya ƙi sa masa hannu domin ya zama doka, to idan ya kai kwanaki 30 ya zama dokar,” inji Minista Bagudu.
Ya ce kuma ai tuni ma su Majalisar Dattawa ta yi wa kasafin na 2024 ƙari, daga Naira tiriliyan 27.5 ɗin da Shugaban Ƙasa ya aika masu, suka maida shi Naira tiriliyan 28.7, ƙarin Naira tiriliyan 1.2 kenan.”
“Lokacin da Shugaban Ƙasa ya gabatar masu da kasafin 2024, Dala 1 ta na Naira 750 ne. Amma sai Majalisar Dattawa ta ƙara gejin zuwa Naira 800 a duk Dala ɗaya. Kun ga hakan zai ƙara samar da kuɗin shiga kenan.”
Discussion about this post