Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya roƙi manyan masu zuba jari na ƙasar Qatar cewa shi gwamnatin sa ba irin gwamnatin baya ba ce, wadda wasu jami’an gwamnati ke karɓar cin hanci kafin su haɗa masu son zuba jari Najeriya da shugaban ƙasa.
Tinubu ya roƙe su cewa ƙofa a buɗe ta ke so shigo Najeriya su zuba jari, domin akwai damammaki sosai na jiran su.
Ya ce duk wani jami’in gwamnati da ya nemi su ba shi cin hanci kafin ya haɗa su da shugaban ƙasa, to su faɗa masa ko wane ne, su fallasa sa shi.
Haka ya sanar a lokacin ganawarsa da Zauren Masu Zuba Jarin Najeriya da Qatar, a Doha, babban birnin Qatar.
“Kada kowa ya bayar da cin hanci don a haɗa shi da ni a Najeriya. Idan wani ya nemi ku ba shi cin hanci, to ku sanar da ni. Haka idan ma ya karɓa, ku faɗa min. Saboda za ku samu damar gani na.
“Yanzu Najeriya ba kamar irin Najeriya ta can baya ba ce, inda ake mana kallon masu son zuba jari ba su iya ganin shugaban ƙasa, sai sun bayar da cin hanci. Saboda haka kada irin waɗannan labarin da ku ka riƙa ji a gwamnatocin baya su kashe maku guyawu.
“Yanzu Najeriya vda gaske ta ke yi, muna ƙoƙarin samar da nagartaccen sauyi ga tsarin zuba jari. Za mu cire duk wasu tarnaƙi da matsalolin da masu sha’awar zuba jari ke fuskanta a Najeriya. Mun yi hakan sosai a cikin watanni tara da muka yi kan mulki.
“Don haka ina tabbatar maku cewa shigowa Najeriya a zuba jari kyauta ne, haka fita ɗin ma kyauta ne. Kuɗaɗen za ku riƙa hada-hada a waje da kuɗaɗen ku a duk lokacin da ku ke so. Saboda haka ku hanzarta zuba jarin ku a Najeriya.”
Discussion about this post