Ɗaya daga cikin shugabannin kamfanin kirifto na Binance da ke tsare a Najeriya bisa tuhumar su da laifin kauce wa biyan haraji da wasu laifuka, ya tsere daga inda ya ke tsare.
Wata ƙwaƙƙwarar majiya ce ta shaida wa PREMIUM TIMES haka, amma ta ce kada a ambaci sunan ta.
Majiyar mu ta ce Anjarwalla, mai shekaru 38 a duniya, ya tsere a ranar Juma’a, 22 ga Maris, daga wani gidan saukar baƙin da jami’an tsaro suka killace shi, tare da ɗaya abokin aikin na sa.
Ya arce ne bayan jami’an tsaron da ke gadin gidan sun kai shi wani masallacin kusa da gidan domin ya yi Sallah, saboda alfarmar watan Ramadan.
Gudajjen wanda ɗan ƙasar Birtaniya ne, kuma ya na da katin shaidar ɗan ƙasar Kenya, an tabbatar da cewa ya tsere tuni ua hau jirgin Middle East air ya fice daga Najeriya.
To sai dai ba a san yadda aka yi har Anjarwalla ya samu tikitin ficewa ba, duk da kuma cewa shi ɗan ƙasar Birtaniya ne, kuma da fasfo na Birtaniya ya shigo Najeriya, kuma fasfo ɗin ya na hannun mahukuntan Najeriya.
Haka kuma wannan jarida ta ji cewa mahukuntan Najeriya na ƙoƙarin gano ƙasar da ya nufa, da niyyar sake kamo shi daga can a maido shi Najeriya.
Wani jami’in shige-da-fice ya ce shugaban na kirifoton Binance ya gudu ne ta hanyar amfani da fasfo na Kenya.
Sannan kuma jami’in ya ce hukumomi na binciken yadda mutumin ya mallaki fasfo na ƙasar Kenya, kasancewa ba shi da wasu takardun fita waje, baya ga na Birtaniya da ke hannun jami’an Najeriya.
Wata majiya kuma ta ce shugabannin na kirifto an tsare su ne “a lafiyayyen gidan saukar baƙi”, kuma an ba su damammaki ciki har da iznin amfani da tarho, wanda ta hanyar tarho ɗin ne ake kyautata zaton Anjarwalla ya kitsa tuggun tserewar sa.
Da aka tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran Mashawarcin Musamman na Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro, Zakari Mijinyawa, ya ce zai bincika sannan ya sake kiran wakilin mu.
Shugabannin na Kirifto biyu dai su na tsare a Najeriya tun bayan zuwan su a ranar 26 ga Fabrairu, 2024.
Asalin Tirka-tirkar Rikicin Najeriya Da Binance:
Gwamnatin Najeriya ta yanka wa kamfanin ‘crypto’ na Binance tarar Dala biliyan 10.
Gwamnatin Najeriya ta nemi kamfanin ‘crypto’ na Binance ya biya kuɗin tara har Dala biliyan 10.
Wannan hukunci na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da binciken zargin da ake wa Binance da sauran kamfanonin ‘yan ‘crypto’ da hannu wajen haifar da masifar tsadar dala a Najeriya.
Mashawarcin Musamman kan Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka, a wata tattaunawa da ya yi da gidan rediyon BBC, a ranar Juma’a ɗin yau.
Ya ce kamfanin Binance ya ci ƙazamar riba daga “hada-hadar biliyoyin dalolin” da ya yi ta haramtacciyar hanya a Najeriya. Yayin da ita kuma Najeriya ta yi mummunar asara, inji Onanuga.
Discussion about this post