Wata sabuwar ƙididdigar da Ofishin Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa ta fitar, ya nuna cewa tsadar farashin kayan abinci da kayan masarufi ya cilla har zuwa ƙaruwa da kashi 37.92 a cikin watan Fabrairu.
Amma malejin tsadar rayuwa a cikin watan Fabrairu ya ƙaru zuwa kashi 31.70, idan aka kwatanta da kashi 29.90 na tsadar rayuwa daga Janairu, kamar yadda NBS ta fitar a ranar Juma’a.
Wannan ƙididdigar ta nuna cewa cikin watan Fabrairu 2024 tsadar rayuwa ta ƙaru da kashi 1.80, idan aka kwatanta da Janairu, 2024.
NBS ta ce hauhawar farashi da tsadar rayuwa sun tashi sosai a 2024, idan aka auna da watan Fabrairu 2023 inda ya ke a kashi 9.79, wanda a wancan lokacin maleji ya na kashi 21.91.
Tuni dai ababen more rayuwa suka gagari talaka, inda su kan su masu hali da masu ƙarfin halin sayen wasu kayan amfanin gida su ka fara haƙura.
A Abuja gwamgwanin madarar ruwa mai kwakwa ya doshi Naira 1000. A Kano da wasu garuruwa da dama mutane da yawa sun haƙura da shan sukari, sun koma shan mazanƙwaila.
Kires na ƙwan ƙanin gidan gona a wasu wuraren ya haura Naira 3,000.
Sai dai kuma wasu na ganin umarnin buɗe kan iyakokin Najeriya da Nijar da kuma cire wa Nijar ɗin dukkan takunkumin Najeriya da na ECOWAS, zai sa a samu sauƙi nan gaba, musamman a Arewa, yankin da ke fama da matsalar tsaro a cikin watan Ramadan.
Discussion about this post