Matatar Fetur ta Ɗangote da ke Legas, ta bayyana cewa za ta kafa sashen hada-hadar sayen ɗanyen mai domin samun ɗanyen mai ɗin da za ta riƙa tacewa har ganga 650,000 a kowace rana.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ce akwai yiwuwar a kafa sashen a birnin Landan, wanda hakan zai a riƙa samun manyan ‘yan kasuwar da za su riƙa sayar wa masana’antar ɗanyen mai da sauran aikatacen da za a buƙata na yau da kullum.
Hakan a cewar Matatar Ɗangote, zai rage kashe kuɗi sosai wajen samun ɗanyen mai da sauran hidindimu na yau da kullum.
Yayin da yin hakan zai sa kamfanin ya rage kashe kuɗaɗe, ganin cewa sabuwar masana’anta ce da ba ta daɗe da fara aiki ba, a gefe ɗaya kuma wannan yunƙurin da Ɗangote ya yi tawaya ce sosai ga manyan kamfanonin hada-hadar ɗanyen mai irin su Vitol da Trafigura, waɗanda majiya ta ce a sun yi hada-hadar cinikayya da Masana’antar Fetur ta Ɗangote.
Yayin da Vitol cinikin ga-wuri-ga-waina kamfanin ya yi da Matatar Ɗangote, shi kuwa Trafigura yarjejeniya ce aka yi idan ya sauke wa Ɗangote lodi, to za a cika masa dukkan jiragen ruwan sa da mai.
Matatar Ɗangote wadda aka kashe Dala biliyan 19 wajen gina ta a Legas, ta fitar da sanarwar neman fitar da mai a watan jiya. Na farko shi ne metrik tan 65,000, sai kuma na biyu tan 60,000.
Majiya ta ce manyan kamfanonin mai na duniya su Vitol, BP da Trafigura sun gana gar-da-gar da Ɗangote, mai mafi ƙasaitar arziki a faɗin Afrika kwanan nan domin bayar da lamunin Dala biliyan 3, wadda ake buƙata domin a riƙa sayo ɗanyen man daga waje.
Sai dai kuma majiya ta ce kamfanonin uku sun nemi a riƙa biyan su bashin da mai, amma kuma a nan zancen ya kwana, saboda Ɗangote na jin tsoron abin da wannan saɓat-ta-juyat-tar yarjejeniya ɗin zai iya haifarwa a ɓangaren maganar riba.
“Ai Ɗangote mutum ne mai dabara, ba zai amince da wayau ɗin su ba,” haka Reuters ta ruwaito wani da ya san komai a lamarin ya tsegunta.
Radha Mohan, wanda shi ne Daraktan Kasuwanci da Shigo da Ɗanyen Mai na Rukunonin Ɗangote Group, ana ganin cewa shi ne zai zama shugaban kamfanin.
Ɗangote ya ce a cikin wannan shekarar matatar za ta riƙa tace daidai adadin ganga 650,000 a kullum. A cikin watan Janairu ne matatar ta fara tace ɗanyen mai.
Discussion about this post