Shugaban kasa Bola Tinubu ya sha alwashin ba zai biya kudin fansa ga Ƴanta’adda da suka sace ɗalibai da ma waɗanda suka sace mutane a sassan kasarnan.
Ministan yada labarai Mohammed Idris, wanda ya bayyana haka a Abuja yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba, ya ce shugaban ya kuma umarci hukumomin tsaro da su tabbatar an ceto duk wadanda aka sace ba tare da biyan kudin fansa ba.
” Shugaba Tinubu ya kuma ba da umarnin cewa babu wani kudin fansa da gwamnati za ta biya wani ɗanta’adda don a sako waɗanda aka sace. Wannan ina su kowa ya sanda haka kuma a sani hakanne matsayar gwamnati.
Idan ba a manta ba a jihar Kaduna, ƴanta’adda sun arce da ɗalibai da malamansu har 300 uku sannan wasu rahotanni ya sake nuna an sace wasu mutum 62 a yankin Kajiru, baya ga na Kuriga.
Haka a jihar Barno, Ƴan bindiga sun sace mata akalla 400 inda suka nausa da su cikin daji.
Rahotanni da PREMIUM TIMES HAUSA bata tantance ba ya ce wai Ƴanta’adda sun nemi a biya su har naira Tiriliyan 40, kuɗin fansan yaran kafin su sako su.
Discussion about this post