Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa akalla mutum 96 sun kamu sannan cutar ta yi ajalin mutum 23 a jihohi 12 a cikin mako daya a kasar nan.
Hukumar ta ce yaduwar cutar ya faro daga ranar 19 zuwa 25 ga Fabrairu wato mako na 8 a shekarar 2024.
NCDC ta ce an samu kari a yaduwar cutar daga mutum 66 a cikin mako na 7 zuwa mutum 96 inda daga cikin su akwai jami’an lafiya shida da suka kamu da cutar.
Hukumar ta Kuma ce daga mako na daya zuwa mako na 8 mutum 573 ne suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 108 a kasar nan.
Bisa ga alkaluman da hukumar ta fitar cutar ta yi ajalin mutum 16.4% a shekarar 2023 sannan a shekarar 2024 cutar ta yi ajalin mutum 18.8%.
Yaduwar cutar
NCDC ta ce cutar ta yadu a kananan hukumomi 93 a jihohi 24 dake kasar nan a Najeriya.
Kashi 64% na mutanen da suka kamu da cutar an gano su ne a jihohin Ondo, Edo da Bauchi sannan sauran kashi 36% a jihohi 21 a kasar nan.
Cutar ta fi kama mutane masu shekaru 31 zuwa 40.
Hukumar ta ce gwamnati ta bada umarnin bude asibitoci domin kula da mutanen da suka kamu da cutar.
Abubuwan da za a kiyaye don gujewa kamuwa da zazzabin lassa
Tsaftace muhalli: A Rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wurare.
Zubar da shara: Idan aka Tara shara kada a rika zubar da shi kusa da gida a rika kaiwa can waje.
Killace Abinci da ruwan Sha: Yin haka zai taimaka wajen hana bere ko kwari shiga cikin abinci ko ruwan sha.
Dafa nama: Kafin a dafa nama kamata ya yi a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.
Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci a inci sannan idan an kammala amfani da ban daki.
Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cuter ya sole su.
Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake Koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.
Wanke gawa a cikin daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ko Kuma a inda ya kamata.
Discussion about this post