Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Wale Edun, wanda kuma shi ne Ministan Lura da Tattalin Arzikin Ƙasa, ya bayyana yadda gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tare da tsohon Shugaban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele suka jefa ƙasar nan cikin masifar raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da shi.
Edun ya shaida wa Kwamitin Lura da Harkokin Kuɗaɗe na Majalisar Dattawa cewa Emefiele ya buga wa gwamnatin Buhari zunzurutun kuɗi har Naira tiriliyan 22.7 tsawon shekaru takwas ya na bai wa gwamnatin ramce.
Ministan ya bayyana hakan a ganawar sa da mambobin Kwamitin Majalisar Dattawa mai Lura da Harkokin Kuɗaɗe, a ranar Laraba, a Majalisa, Abuja.
Cikin watan Mayu 2023 ne Majalisar Dattawa ta ruguguta amincewa gwamnatin Buhari ta ciwo bashin Naira tiriliyan 22.7 daga CBN.
Majalisar ta yi hakan ne bayan Fadar Shugaban Ƙasa na lokacin, Buhari ta nemi amincewar, a cikin wasiƙar neman amincewa da Buhari ya aika majalisar.
Buhari ya aika wa majalisa wasiƙar neman amincewar, bayan tuni ya rigaya ya shafe shekaru takwas ya na karɓar basussukan ba tare da neman amincewar Majalisar Dattawa ba.
Ya rubuta wasiƙar neman amincewar, kwanaki kaɗan kafin saukar sa daga mulki, domin a ajiye ta matsayin shaida ko hujjar cewa da izinin majalisa ya riƙa karɓar kuɗaɗen, duk kuwa da cewa sai bayan an gama karɓar kuɗaɗen ne aka aika wa Majalisa domin ta amince a rubuce.
Minista Edun ya dai shaida wa kwamitin majalisa cewa riƙa buga kuɗaɗen barkatai tsawon shekaru takwas da CBN ya riƙa yi zamanin Buhari, shi ne musabbabin tashin hankalin raɗaɗin tsadar rayuwa da raɗaɗin kwankwatsar da tattalin arzikin Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.
“Wannan masifa da ake ciki ta samo asali ne daga yadda CBN a ƙarƙashin Godwin Emefiele ya riƙa buga wa gwamnatin Buhari kuɗaɗe har Naira tiriliyan 28 da sunan ramce.”
Wani abin damuwar da Minista Edun ya nuna, shi ne inda ya ce gwamnati za ta riƙa tatsar kuɗaɗen haraji domin ta tara Naira tiriliyan 7 domin ta biya CBN, kamar yadda majalisa ta yi umarni.
Dama tun cikin makon shekaranjiya Majalisar Dattawa ta ɗora laifin matsalar da ake fama da ita, cewa ta samo asali ne tun da CBN ya ramta wa gwamnatin tarayya Naira tiriliyan 22.7 a zamanin Buhari.
Discussion about this post