Wani likita mai suna Dr Ken ya yi kira ga maza da su rika yin jima’i akalla sau 21 a wata domin samun kariya daga kamuwa da cutar dajin dake kama ‘ya’yan mairainai.
Ken ya fadi haka ne da yake hira da shirin kafar radiyo na ‘Classic FM, 97.3.’
A Shirin dake ta taken ‘A tattauna’ Ken ya shawarci mazaje da su kara yawan lukuttan saduwa da iyali domin kaucewa kamuwa da irin wannan cututtuka.
Cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraina cuta ce dakan hana namiji yin fitsari da kuma wasu illoli masu yawa. Idan ba a maida hankali a kai ba sai ka ga har an rasa rai.
Cutar ya fi kama maza masu shekaru 40 zuwa sama.
Binciken Dubawa da Abin da likitoci suka ce.
Dubawa ta gudanar da binciken domin gano ko akwai gaskiya a bayanan da Ken ya yi.
Sakamakon binciken da gidauniyar ‘Urology Care’ ta gudanar a 2004 kan amfanin yawan fitar da maniyi ga namiji ya nuna cewa mazan dake yawan fitar da maniyi a jikinsu na samun kariyar kashi 20% na gujewa kamuwa da dajin dake kama ya’yan marainan.
Duk da haka gidauniyar ta ce za ta zurfafa gudanar da bincike a kai domin samun Karin haske.
Wani sakamakon binciken da aka gudanar a 2016 ya nuna cewa yawan fitar da maniyi ga namijin da ya dara shekaru 50 na kare shi daga kamuwa da cutar sai dai kuma yana cutar da matasa yan kasa da shekaru 20 zuwa 40.
Sauran abubuwan da ka iya haddasa cutar sun hada da rashin cin abincin dake inganta garkuwar jiki, zukar taba sigari, Shan giya, rashin motsa jiki, ana iya gadon cutar da dai sauran su.
Wani likitan mata Jeremiah Agim ya ce babu alakan yawan yin jima’i ko yawan fitar da maniyi da samun kariya daga kamuwa da cutar dajin ya’yan maraina.
Ya ce akwai wasu abubuwan dake haddasa cutar a jikin namiji da suka hada da shekaru da irin rayuwar da mutum ke yi da jin rauni a ‘ya’yan maraina.
Ogundunniyi ya ce a baya mutane sun yi zaton cewa kamuwa da cutar sanyi shine ke hadasa dajin ‘ya’yan maraina sai dai kuma har zuwa yanzu babu sakamakon binciken da suka tabbatar da haka din.
A takaice dai Dubawa ta yanke hukuncin cewa fitar da maniyi na taimaka wa mazan da suka dara shekaru 50 daga kamuwa da cutar amma yana cutar da maza matasa masu shekaru 20 zuwa 40.
Duk da hakan Dubawa ta ce wannan batu ne da ya kamata a zurfafa gudanar da bincike a kai domin samun Karin haske.
Discussion about this post