Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin a buɗe duka rumbunan abunci dake Najeriya domin wadata talakawa da abinci a ko ina a faɗin kasar nan.
Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya bayyana haka da yake hira da manema labarai a fadar shugaban kasa ranar Alhamis.
” Mun tattauna yadda za a kawo karshen matsalar yunwa da tsananin rashin abinci da ƴan Najeriya ke fama da shi. Za a buɗe rumbuna, za a siyo abinci a raba wa talakawa. Sannan kuma idan bai isa ba gwamnati zata siyo daga waje.
Discussion about this post