Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Alhamdulillah, alhamdulillah, alhamdulillah. Yau ranar laraba, 07/02/2024, mun wayi gari da wani kyakkyawan labari daga Kano; labari mai dadin ji; labarin farin ciki da murna a wurin duk wani mutum mai gwagwarmayar tabbatar da gaskiya da adalci a bayan kasa; labarin da duk wani mutum mai kaunar gaskiya da masu gaskiya a duk inda suke a duniya sai so yaji.
Cewa wata kungiya a jihar Kano ta yi kira da a rusa wasu masarautun karya, masarautun caka; masarautun da dama can an kirkiro su ne bisa rashin gaskiya, bisa zalunci, bisa rashin adalci, da kuma nufin raba kan al’ummar jihar Kano tare da raunata masarautar da mayar da ita baya, sannan a mayar da Mai Martaba Khalifah Sarki Muhammad Sanusi na II a matsayin sabon sarkin Kano na goma sha shida.
Kungiyar mai suna ‘Yan Dangwalen Kano ta bukaci mai girma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da majalisar dokokin jihar da su duba sashen dokar da ta tsaga masarautar Kano zuwa masarutu biyar.
Kungiyar ta ce masarauta guda daya kamar yadda take a can baya, tabbas shine zai taimaka wajen tafiyar da harkar sarauta ba tare da rarrabuwar kai ba. Sannan hakan zai samar da zaman lafiya, da ci gaba da hadin kai mai dorewa.
Dangane da Mai Martaba sarki Muhammad Sanusi II, kungiyar ta ce suna kira ga majalisar dokokin jihar Kano, da tayi waiwaye dangane da sashen dokar da ya cire Sarki Muhammad Sanusi II daga karagar mulki. Suka ce sun yi amannar cewar cire Sarki Muhammad Sanusi II ya haifar da rashin zaman lafiya, rashin hadin kai, kiyayya da gaba a jihar.
Daga karshe kungiyar ta bukaci majalisar dokokin da ta yi duba kan bukatunta domin ci gaba tare da karuwar arzikin al’ummar jihar Kano baki daya.
To a gaskiya ina mai tabbatar maku, duk al’ummar jihar Kano, masu nufin jihar da alkhairi suna tare da ra’ayin wannan kungiya ta ‘Yan Dangwale dari-bisa-dari.
Kai bama al’ummar jihar Kano kawai ba, duk wani Dan Najeriya, mai nufin jihar Kano da Kanawa da alkhairi; mai son ci gaban jihar Kano da zaman lafiyar ta da hadin kan ta, wallahi zai goyi bayan wannan kungiya mai albarka ta ‘Yan Dangwale. Da haka ake samun kungiyoyi suna dangwalo wa al’ummominsu alkhairi da ci gaba, ai da kasar mu ta gyaru!
Duk mai bin kafafen yada labarai na gida da na waje, da jaridu daban-daban, da soshiyal midiya, wallahi zai ga cewa, al’ummar jihar Kano baki daya, suna tare da Mai Martaba Khalifah Sarki Muhammad Sanusi II ne. Kuma suna son sa, suna kaunar sa tsakaninsu da Allah, kuma suna goyon bayan dawowarsa a matsayin Sarkin su na Kano dari-bisa-dari.
Kai hasali ma, mun tattauna da dubban Kanawa, sun tabbatar muna da cewa, ko gwamna Abba Kabir Yusuf ma, daya daga cikin dalilan da yasa suka zabe shi, suka bashi kuri’unsu, shine ya dawo masu da Sarki Muhammad Sanusi II gidan Dabo.
Kuma in dai har Dimokradiyyah ita ce, yiwa mutane abun da suke so matukar shine daidai, to ya zama dole, tilas, kuma wajibi, gwamna Abba Kabir Yusuf ya saurari koken Kanawa, ya dawo masu da Sarki Muhammad Sanusi II akan karagar sarautar gidan Dabo. Domin duk wani shugaba da al’ummah suke so, kuma suke kauna, to shine alkhairi ga kowa da kowa. Kuma shine kadai zaku iya yin aiki tare, ya baka cikakken hadin kai da goyon baya, domin kawowa Kanawa alkhairi da ci gaba mai amfani.
Imam Ahmad da Imam Muslim sun fitar da wani Hadisi na Auf Bin Malik Al-Ashja’i, Allah ya kara masa yarda yace:
“Naji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Mafiya alkhairin shugabanninku sune wadanda kuke so suke son ku, kuke kaunarsu suke kaunar ku, kuke yi masu kyakkyawar addu’a da fatan alkhairi, su ma suke yi maku. Sannan mafiya sharrin shugabanninku sune, wadanda baku son su suma basa son ku; baku kaunarsu suma basa kaunarku; wadanda kuke zagi da la’anta su ma suke zagin ku da la’antar ku…”
Kun ga wannan ya nuna kenan, shugabannin da al’ummah suke so, suma suke son su, wadanda suke kauna, suke kaunarsu, sune kadai idan suka hadu suka yi aiki tare, zasu zamar wa al’ummah alkhairi.
Kuma sannan kowa ya sani, wallahi tun farko an cire Sarki Muhammad Sanusi II ne a bisa zalunci da rashin adalci. Kuma a lokacin duk wani mai cikakken hankali, mai ilimi, mai basirah da hangen nesa yayi wa Ganduje magana akan kar yayi wannan irin ganganci, kar yayi wannan aika-aika, amma a lokacin giyar mulki ta hana Ganduje ya saurare su, kuma yayi watsi da duk wasu kiraye-kiraye da ake yi masa akan hakan. Ya toshe kunnuwansa, yaki jin maganar malamai, yaki jin maganar ‘yan uwansa ‘yan siyasa, yaki jin maganar manya da dattawan arewa baki daya.
Kuma mu a lokacin, mun fada masu gaskiya, shi da magoya bayansa masu zuga shi. Muka ce masu, su je su bincika, a tarihin duniya, zalunci bai taba dorewa ba.
Su fada muna, a ina ne zalunci ya taba dorewa?
Kuma mun fada masu, in dai giyar mulki ce ina su Fir’auna? Meye basu yi ba? Wane irin mummunan abu ne giyar mulki ba ta sa su sun aikata ba? To amma yau ina suke? Duk sun zama tarihi. Kuma tarihi mummuna, ba mai kyau ba!
Kuma wai ma idan ba rashin hankali da toshewar basirah ba, don Allah, don Allah, don Allah ta yaya gwamna Abba Kabir Yusuf ma zai iya yin aiki, ko yaji dadin yin aiki da mutanen da kowa yasan da cewa basu son sa, kuma basu kaunarsa?
Duk duniyar nan tana sane, kuma duniya ta shaida irin adawar da wadannan mutane masu suna “sarakuna” suka nuna wa gwamna Abba Kabir Yusuf. Adawa da rashin kauna a fili karara. Tun lokacin zabe har zuwa maganar shari’un da aka yi a kotuna, duk sun taka rawa akan kar Abba Kabir Yusuf ya tabbata gwamnan jihar Kano. Kuma saboda rashin hankali, sai ace wannan mutum ya kyale su, ya bar su kar ya sauke su? Idan ma har yayi hakan to ya tabbata marar ilimi kenan!
Ta yaya ma mutumin da baya tare da kai, bai so zaman ka gwamna ba, har zai baka hadin kan da zaku yi aiki tare, domin ci gaban al’ummah? Sam ba zai yiwu ba!
Don haka yanzu dai ya rage ga gwamna Abba Kabir Yusuf da ‘yan majalisar jihar Kano. Ya zama tilas su dubi waccan bukata, ta wannan kungiya ta ‘Yan Dangwale, suyi wa Kanawa abun da yake shine daidai.
Kuma wallahi ina kalubalantar duk wani mutum da yake ganin cewa akasin haka shine daidai, da ya fito, tsakaninsa da Allah, ba tare da wani son zuciya ba, ya fada muna wani shugaba, tun daga shugaban kasa, har zuwa gwamnoni, kai ko ma wane irin shugaba ne, wanda zai iya yin aiki tare da mutanen da yasan cewa basu son sa, basu kaunarsa. Mutanen da suka nemi su tadiye masa kafafu, su kunyata shi. Wadanda suka nuna masa adawa a fili karara. Suka hada kai da makiyansa wurin yakarsa!
Sam ba za’a taba samun shugaban da zai kyale irin wadannan, har yayi aiki tare da su ba. Domin wallahi ko ya bar su, to zasu ci gaba da yi masa makirci, da yankan baya, da zagon kasa ne!
Masarautar Kano, kafin Ganduje yayi mata aika-aikar da yayi mata, duk duniya ta shaida cewa masarauta ce mai karfin gaske; Masarauta ce mai cike da kwarjini da mutunci, to amma don Allah, don girman Allah, bayan Ganduje yayi mata lahanin da yayi mata, ya gutsutstsurata, yaya ta dawo? Mu fadi gaskiya fa, domin zamu tsaya gaban Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi muna hisabi gobe alkiyama!
Yaya masarautar Kano ta dawo yau???
A da can kafin Ganduje yayi mata lahani, da ance ga Sarkin Kano nan, yaya kake gani?
Amma a yau idan ance ga Sarkin Kano nan, wa ma ya damu da ya gan shi?
Haba jama’ah! Me yasa don girman Allah har ake samun wasu mutane a cikin wannan al’ummah da basa son gaskiya ne? Me yasa idanuwan mu suke makancewa daga ganin gaskiya ko fahimtar gaskiya?
Don haka, muna kira ga Kanawa da su shirya FATAHU KANO da yardar Allah. Allah zai dawo masu da martabar su da Allah ya basu ta bangaren sarauta In Shaa Allahu!
Kuma mu sani, kar mu yarda mu saurari duk wani mashirmaci cikin al’ummah. Ya zama dole mu goyi bayan gaskiya, kuma mu kasance tare da masu gaskiya a koda yaushe kuma a duk inda muke.
Mu zama masu fadin gaskiya komai dacinta, kai ko da akan kawunan mu ne, ba tare da jin tsoron wani ko shakkarsa ba!
Allah ya jikan Malam Sa’adu Zungur, ya gafarta masa, amin.
Ya kasance a cikin wani wake nasa yana cewa:
“GASKIYA KU FADE TA KOMAI DACI, KAI KO DA ZA’A CE WANE YAI GANGANCI.”
Kamar yadda muka sani, ana jagoranci ne da duk wani shugabanci domin kawowa al’ummah ci gaba da amfani ta fuskoki daban-daban. To idan kuwa haka ne, tabbas ba zaka taba hada Khalifah Sarki Muhammad Sanusi II da duk wadancan mutanen, wurin kawowa al’ummar jihar Kano ci gaba ba. Kowa yasan da wannan, amma sai dai son zuciya ya hana mu yarda da hakan ko fahimtar hakan!
Idan kuma abun ya zama haka, to sai dai muce Allah ya sawwake, kuma ya raba mu da bin son zuciya, amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam a lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post