Tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin Soja, kuma ɗaya daga cikin shugabannin da suka kafa ECOWAS cikin 1975, ya yi kira ga ƙungiyar ta ƙasashen Afrika ta Yamma cewa ta cire takunkumin da ta ƙaƙaba wa ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.
Ya ce “Dukkan shugabannin ƙasashen Afrika ta Yamma su maida hankali wajen gaggauta cire da ƙasashen uku takunkumi.”
Gowon da ya na cikin shugabannin da suka kafa ECOWAS cikin 1975, lokacin ya na shugaba na mulkin soja.
Ya nuna damuwar sa dangane da abubuwan da ke ta faruwa a cikin ƙasashen ƙungiyar ta ECOWAS.
Ya bayyana hakan cikin wata wasiƙa da ya aika wa dukkan Shugabannin Ƙasashen ECOWAS.
Ya rubuta wasiƙar dai a ranar 13 ga Fabrairu, kamar yadda PREMIUM TIMES ta ci karo da ita a ranar Laraba ɗin nan.
Ya rubuta wasiƙar mako ɗaya bayan Mali, Nijar da Burkina Faso sun ayyana ficewar su daga ECOWAS, su na yi wa ƙungiyar zargin cewa ta tashi daga kare muradun ƙasashen Afrika ta Yamma, ta zama ‘yar amshi Shatan Turawan Yamma, musamman ma ƙasar Faransa.
An dai ƙaƙaba wa ƙasashen uku takunkumi ne bayan sun kifar da gwamnatin farar hular ƙasashen.
Giwon ya ce abin ya na baƙanta masa rai ganin yadda rashin haɗin kai tsakanin ƙasashe ke neman kekketa rigar mutuncin ECOWAS, bayan ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso daga ECOWAS.
Ya ce rashin haɗin kai tsakanin ƙasashen ECOWAS da kuma takunkumi zai illata talakawa ne kaɗai, waɗanda an kafa ƙungiyar ce domin amfanin haɗin kai da zamantakewa tsakanin su.
Gowon ya kuma roƙi ƙasashen uku da suka fice da su koma cikin ƙungiyar. Kuma ya yi kira da a gaggauta taron ECOWAS kan batun matsalar tsaro, zaman lafiya da arzikin yankin da kuma rawar da ƙasashen Turai ke takawa a yankin.
Discussion about this post