Ana cikin halin fargabar tashin-gwauron-zabin Dala a Babban Bankin Najeriya (CBN), yayin da ake zaman kasafta wa gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi kason kuɗaɗen ƙarshen wata.
A duk ƙarshen wata dai ɓangarorin gwamnatocin uku na zaman kasafta kuɗaɗen shigar da gwamnatin tarayya ke samu daga haraji da riba.
PREMIUM TIMES ta ji daga wata majiya cewa sau da yawa idan an kasafta kuɗaɗen, wasu gwamnoni na canja nairorin da aka ba su na jihar su zuwa daloli, lamarin da harƙalla ce kuma rashawa ce, sannan kuma dokar Najeriya ta haramta irin wannan wala-walar.
Ranar Laraba dai PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa Gwamnatin Najeriya ta toshe kafar cinikin kuɗi na tsarin Binance, wanda da Hausa ake kira ‘yan kiripto.
An yi zargin su ne ke amfani da manhajar su su na ƙara wa dala daraja.
Majiya a cikin manyan kamfanonin sadarwa sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin toshe hanyoyin hada-hadar kuɗaɗe ta Binance nan take.
Baya ga Binance, sauran waɗanda aka hana sun haɗa da Forextime, OctaFX, Crypto, FXTM, Coinbase da Kraken da wasu daban.
Sashe na 165 na Dokar Najeriya da Dokar Rabon Kuɗaɗen Tarayya Mai Lamba 1 ta 1982, ta bayyana cewa kuɗaɗen shigar da gwamnatin tarayya ke tarawa a riƙa killace su cikin Asusun Gwamnatin Tarayya, sai ƙarshen wata a kasafta su tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
Akwai Kwamitin Kasafta Kuɗaɗen Tarayya wanda shi ne ke da alhakin raba waɗannan kuɗaɗen.
Kwamitin ya ƙunshi Kwamishinan Kuɗaɗe na kowace jiha, wakilai daga Ofishin Akanta Janar na Tarayya da kuma Akanta Janar na kowace jiha.
Ministan Harakokin Kuɗaɗe ne Shugaban Kwamiti. Akwai wakilai daga Babban Bankin Najeriya, CBN, Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe, Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare da kuma Ofishin RMAFC da sauran su.
Gwamnatin Tarayya na karɓar kashi 52.68 na jimlar kuɗaɗen, sai a bai wa jihohi kashi 26.72, sai kuma ƙananan hukumomi a ba su kashi 29.60.
Kuɗaɗen ne ake biyan albashi da su a tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi. Sai kuma biyan ayyukan raya ƙasa da sauran hidindimu tafiyar da gwamnati.
Cikin Janairu 2024, sun raha Naira tiriliyan 1.127 tsakanin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi. A cikin Disamba 2023 kuwa, Naira tiriliyan 1.783 suka kasafta a tsakanin su.
Tsoron Abin Da Ka Iya Biyo Baya:
Majiyoyi daban-daban sun shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Alhamis cewa masu leƙen asiri sun gano a duk lokacin da ake wannan rabon kuɗi, to darajar Naira na faɗuwa warwas.
Ana zargin cewa wasu gwamnoni na karkatar da kuɗaɗen jihar su zuwa Dalar Amurka a kasuwar ‘yan canji a duk lokacin da suka karɓi kason su daga kaɓakin gwamnatin tarayya.
Discussion about this post