Gwamnatocin ƙasashen Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso za su kafa tarayyar ƙasashen zumunta, bayan ficewar su daga ECOWAS.
Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnatin Mali ya bayyana cewa manyan jami’an diflomasiyyar mu sun bai wa shugabannin mu shawarar kafa Tarayyar Ƙasashe Uku, wadda zata ƙunshi Nijar, Mali da Burkina Faso,” inji Abdoulaye Maiga, a ranar Alhamis a shafin sa na Facebook.
Kanar Maiga ya yi wannan furuci ne yayin taron ministocin ƙasashen uku, a Ouagadougou, babban birnin ƙasar Burkina Faso.
Maiga shi ne Ministan Kula da Mali, ya ce an bayar da wannan shawara ta kafa ƙungiyar ƙasashen uku ne tun cikin Nuwamba 2023 yayin taron su.
Kuma sun yi bayanin cewa za su miƙa tayin faɗaɗa yawan ƙungiyar ga wasu ƙasashen Sahel, kungiyar da aka ƙirƙira cikin Satumba, 2023, wata ɗaya bayan juyin mulkin Nijar.
Ƙarshen watan Janairu ne ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso sun fice daga ECOWAS bayan ɗaukar tsawon watanni ana kai ruwa da Nijar.
Ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun bayyana ficewar su daga Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS.
Ƙasashen uku dai su na ƙarƙashin mulkin soja ne, bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da shugabannin fararen hula a ƙasashen, inda Nijar ce ta baya-bayan nan.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito Shugabannin ƙasashen uku sun zargi ECOWAS da rashin tausayin bil-Adama, biyo bayan takunkumin da aka ƙaƙaba masu.
Cikin wata sanarwar haɗin-guiwa da suka fitar, wadda aka aka watsa a gidajen talbijin na ƙasashen uku, sun ce “mun yanke shawarar tsayawa da ƙafafuwan mu, bisa doron ‘yancin mu. Don haka mun ayyana ficewar mu daga ECOWAS, saboda ƙungiyar ta kauce daga bin kyawawan manufofin da waɗanda suka kafa ta suka ɗora ta a kai, bayan shekaru kusan 50 da kafuwar ta.
“Haka kuma ECOWAS ta bi son ran wasu ƙasashen Turai, har ƙungiyar ta zama barazana ga ɗimbin al’ummar mambobin ƙasashen ta, waɗanda aka kafa ta domin ta faranta masu, ba don ta faranta wa Turawan Yamma ba.”
Ƙasashen sun fice ne bayan watannin da aka ɗauka ana kwan-gaba-kwan-baya don ganin an dawo da mulkin farar hula a ƙasashen uku.
ECOWAS ta ƙaƙaba masu takunkumi kuma har yanzu kan iyakokin Najeriya da Nijar a rufe su ke, kuma an yanke wutar lantarki daga Najeriya zuwa Nijar.
An dai shirya yin taron Ministocin Harkokin Wajen ECOWAS a Yamai, babban birnin Jamhuriyar a ranar 25 ga Janairu, amma abin bai yiwu ba.
“Tawagar ECOWAS ta yini cur a filin jirgin saman Abuja zuwa Nijar, amma daga baya aka sanar cewa “jirgin da zai ɗauke su ya samu matsala.”
Discussion about this post