Kamfanin Ɗangote Group, wanda ya ƙunshi dukkan masana’antu da kamfanonin Ɗangote, ya fallasa yadda Hukumar EFCC ta tada ƙura ba gaira ba dalili, domin ta tozarta kamfanin a idon jama’a.
Dambarwa tsakanin Rukunin Kamfanonin Ɗangote da EFCC dai ta taso ne daga ranar 6 ga Disamba, 2023, ranar da EFCC ta aika wa kamfanin wasiƙar neman dukkan bayanan adadin hada-hadar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje da CBN ya bai wa Kamfanonin Ɗangote, daga 2014 zuwa yau. An dai rubuta wannan wasiƙa ga kamfanoni 51.
Cikin sanarwar da Ɗangote Group ya fitar a ranar Lahadi, ya sanar da cewa jami’an kamfanin Ɗangote da kan su suka ɗauki kwafe-kwafen takardun bayanan da EFCC ta nemi a ba su, suka kai ofishin EFCC a ranar 4 ga Janairu.
“Amma abin mamaki da al’ajabi, sai EFCC suka ce wai ba za su karɓa ba, su da kan su za su je Hedikwatar Kamfanin Ɗangote su karɓa.
“Kawai daidai lokacin da jami’an kamfanin Ɗangote ke can ofishin EFCC, sai kawai aka gayyar jami’an su sun darkako cikin Hedikwatar Kamfanin Ɗangote, wai sun je su karɓi kwafen bayanan da ga su can fa an kai masu har ofis, amma su ka ƙi karɓa.
“Abin da suka yi ya tada ƙura a cikin Najeriya da duniya baki ɗaya, don kawai su jawo mana hankulan mutane a kan mu.
“Ya kamata a fahimci abin na EFCC duk tada ƙura ce ta ba gaira babu dalili, domin da suka dira Hedikwatar Rukunin Kamfanonin Ɗangote don su karɓi kwafen takardun bayanai, ba su tafi da ko fallen takarda ɗaya ba, domin an rigaya an kai masu kwafen takardun tun kafin su kawo caffar dira hedikwatar mu.”
A kan haka ne Rukunin Kamfanonin Ɗangote ya ke kwantar wa dukkan masu ruwa da tsaki a rukunin kamfanonin da masu hannayen jari, cewa su kwantar da hankalin su.
“Tilas mu ƙara jaddada cewa babu wani kamfanin Ɗangote da ke ƙarƙashin Rukunonin Kamfanonin Ɗangote da ya aikata ba daidai ba. A yanzu dai abin da kawai muke yi shi ne taimakon EFCC da bayanan da suke nema daga wajen mu, dangane da binciken da suke kan yi.”
Rukunin Kamfanonin Ɗangote ya ƙara da cewa zai ci gaba da hada-hadar kasuwancin sa domin ƙara bunƙasa tattalin arzikin ƙasa a cikin gida Najeriya.
“Tuni mun bai wa EFCC kwafe-kwafen farkon bayanai, kuma muna ci gaba da aikin tattara sauran bayanai, waɗanda za mu damƙa masu, da zaran mun kammala tattarawa.
“Kada a manta Rukunin Kamfanonin Ɗangote shi ne kamfanin da ba na gwamnati ba wanda ya fi taimaka wa tattalin arzikin Najeriya, kuma shi ne ya fi kowane kamfani ɗaukar ma’aikata masu yawa a ƙasar nan. Kuma ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da aka amince wa jula-jular canjin Kuɗaɗen Waje a Najeriya. Sannan Ɗangote Group ya fi kowane kamfani biyan haraji mafi yawa ga gwamnatin Najeriya.”
Discussion about this post