Gwamnan Kaduna Uba Sani ya sha alwashin bi wa Almajirin da malamin sa ya kusa kashe shi da duka saboda wai bai iya karatu ba.
Da yake jawabi a lokacin karbar yaron a fadar gwamnatin Kaduna wanda kuma dan asalin jiharne, Gwamna Uba Sani ya sha alwashin gurfanar da malamin makarantar Almajirin da laifin aikata mummunar laifi. Ya jaddada cewa babu wani sashe na Alkur’ani da ke goyon bayan azabtar da yara kanana irin haka.
Muazu, tare da wasu yara daga makarantun Almajirai makamantansu da suka fuskanci cin zarafi, an dawo da su Kaduna daga jihar Neja. Gwamnan ya bayyana cewa yaran da aka dawo da su gida ciki har da Muazu za a basu ilimi kyauta a karkashin tsarin ilimin Tsangaya a jihar Kaduna.
“Mun dawo da dukkan yaran daga jihar Neja. Muna da ingantaccen tsarin Tsangaya a Jihar Kaduna inda za mu ba su ilimin addinin Musulunci da na boko. Babu wani wuri a cikin Alkur’ani mai girma da ya ce sai an dauke yara masu karancin shekaru daga kulawar iyayensu kafin su samu ilimin addinin Musulunci. Ba ma son ganin yara suna yawo a titi suna bara,” Gwamna Uba Sani ya tabbatar.
A cikin makon Jiya ne wani malamin makarantar Aljirai a Neja ya ci zarafin wadi dalibin sa inda ya yi masa duka kamar zai kashe shi saboda wai bai yi biya karatunsa ba.
Discussion about this post