Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Canji da ke Zone 4, Abuja, Abdullahi Dauran, ya bayyana cewa a ranar Alhamis za su rufe kasuwar hada-hadar canjin, har sai yadda hali ya yi.
Da ya ke hira a taron manema labarai, a ranar Laraba, Dauran ya ce tsadar masifar da Dala ta yi ne ya sa tilas za su daina hada-hadar, har sai Naira ta wadata, kuma ta ɗan sauko tukunna.
Ya ce babban dalilin ƙarancin Naira, musamman a Najeriya shi ne masu hada-hadar tasarifin kuɗaɗe ta intanet, wato masu irin hada-hada irin ‘kirifto’, wato hada-hadar ‘binance’ da ke zafi a yanzu.
Dauran ya ce muddin Babban Bankin Najeriya (CBN) bai haramta tsarin ‘binance’ ba, to Dala ba za ta taɓa wadata a hada-hadar Najeriya ba, ballantana kuma ta sauka.
Dauran ya nuna damuwa kan yadda aka sayar da Dala 1 har Naira 1,520 a kasuwar ‘yan canji, sannan kuma Naira 910 a farashin gwamnati.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa ta sha ƙwaya, ta na kusa da durƙusar da Najeriya.
Darajar Naira ta yi zubewar da ba ta taɓa yi ba a tarihi, inda a ranar Talata aka sayar da Dala 1 kan Naira 1,482 a kasuwar ‘yan canji.
Lamarin ya yi munin da sai da ta kai har Naira 1,491 duk Dala 1.
A ranar Talata ɗin an riƙa neman Dala wurjanjan a kasuwannin ‘yan canji, lamarin da ya sa ta tsada sosai.
An saida Dala 1 kan N1,490.514. Fam na Ingila kuma N1,855.291. Yuro 1 kan Naira 1,585.719.
CBN ya ɗora laifin faɗuwar darajar Naira kan ƙarancin Dala da kuma yadda ake ci gaba da neman Dala ɗin afujajan kuma wurjanjan.
Wanan jarida ta bada labari yadda tun a ranar Litinin Dala ta lollotsa wa Naira kumatu, ta gaggaɓe mata haƙoran gaba.
Sakamakon rage darajar Naira da Babban Bankin Najeriya ya yi, da nufin samun wadatar Dala a hada-hadar ƙasar nan, darajar Naira ta yi mummunar faɗuwa, inda a kasuwar ‘yan canji sai da aka riƙa sayen Dala ɗaya kan Naira 1,447 a ranar Litinin.
Bayanan ƙididdigar da FMDQ ya fitar ya nuna cewa amma dai a ƙarshe yammacin Litinin ɗin kafin tashi daga kasuwa, Dala ɗaya ta koma daidai da Naira 1,348 a kasuwar ‘yan canji a ranar Litinin ɗin.
Naira na ci gaba da fama da rashin daraja a kasuwar ‘yan canji sanadiyyar neman Dala da ake yi ruwa-a-jallo domin a saya.
Yawancin masu neman dala wurjanjan ɗin su na yi ne domin su sayi daloli su biya kuɗaɗen shigo da kayan da suka yi oda daga ƙasashen waje, biyan kuɗin karatun yaran su da ke karatu a ƙasashen waje, biyan kuɗin tikitin jirage zuwa ƙasashen waje da sauran buƙatun da ake biya da kuɗaɗen Dala ko Fam na Ingila ko Yuro na Gamayyar Ƙasashen Turai ta Yamma.
Naira ta ƙara shiga jula-jula tun bayan da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Cardoso ya ce “mun karya darajar Naira don mu samu shigowar ɗimbin daloli a hada-hadar Najeriya”.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa darajar Naira ‘ta faɗi warwas”.
Cardoso ya bayyana haka a ranar Laraba, wurin Taron Majalisar Ƙolin Tattalin Arzikin Ƙasa (NESG) 2024.
“Mu na da yaƙinin cewa a yanzu darajar Naira ya ragu sosai, kuma hakan wasu matakai ne da aka ɗauka a ɓangaren hada-hadar kuɗaɗe domin samar da farashin kankankan nan gaba kaɗan.
“Wannan tsari da muka bijiro da shi, zai taimaka wajen samar da farashin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje wanda zai wanzar da daidaito,” inji Cordoso.
Kwanan nan dai darajar Naira ta faɗi warwas inda ake sayar da Dala 1 kan Naira Naira 1,372 a kasuwar ‘yan canji.
A farashin gwamnatin tarayya kuma ana Dala 1 na Naira 878.
Cardoso ya ce yin hakan zai samar da daidaiton farashin canji, kuma zai samar da ƙarin samun daloli ta hanyar haɗa hannu da Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe da kuma NNPCL domin ƙarfafa hada-hadar Dala a cikin ƙasa.
Discussion about this post