Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin kasafin kudin shekarar 2024 na Naira Tiriliyan 28.78 ya zama doka.
Shugaban ya sanya hannu kan kudirin dokar ne a ofishinsa dake fadar gwamnatin tarayya Abuja, ranar Litinin
Wadanda suka halarci bikin rattaba hannun, akwai shugaban majalisar dattawa, Goodswill Akpabio; Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudden; Ministan Kudi da kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun; da kuma ministan kasafin kudi da tsare-tsare tattalin arziki, Abubakar Bagudu.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da kasafin kudi Solomon Adeola, da takwaransa na majalisar, Abubakar Bichi da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.
Majalisar dokokin kasar ta zartar da kasafin kudin ne a wani zama na musamman a ranar Asabar.
‘Yan majalisar sun kara kasafin kudin daga Naira tiriliyan 27.5 da shugaban kasa ya gabatar a watan Nuwamba zuwa Naira tiriliyan 28.7, sabanin Naira tiriliyan 1.2.
Yayin da aka rattaba hannu a kan kasafin, gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da tsarin kasafin zartar da kudi daga Janairu zuwa Disamba wanda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata ta fara.
Discussion about this post