Kotun Koli ta tabbatar wa gwamnan Zamfara, Dauda Lawal na Zamfara kujerar sa na gwamnan jihar.
A hukuncin da kotun Koli ta yanke a ranar Juma’a ta ce kotun Ɗaukaka kara sun tafka shirme a hukuncin da suka yanke da cire gwamnan da kuma sanar da sake zaɓe a wasu kananan hukumomi.
Maisharia Emmanuel Agim wanda ya karanta hukuncin a madadin alƙalan kotun ya bayyana cewa kotun ɗaukaka kara ba ta yi abinda ya dace ba ” Sabida haka kotun koli ta jaddada wa Lawal kujerar sa na gwamna Zamfara.
Discussion about this post