Rundunar Sibul Difens NSCDC dake jihar Kano ta bayyana cewa ma’aikatan ta sun kama wani matashi Alkasim Ya’u mai shekara 25 bisa zargin aikata laifin kisan kai.
Shugaban rundunar na jihar Mohammed Falala ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Lahadi a garin Kano.
Falala ya ce wannan abu ya auku ne a Tudun Yola ‘C’ dake karamar hukumar Gwale ranar Juma’aa gidan wani Salisu Bala.
Ya ce mahaifin matashin Alhaji Ya’u Mohammed a ranar 6 ga Janairu ya kawo dansa Alkasim Ya’u wanda ke fama da tabuwar hankali asibitin mahaukata dake Dawanau domin ganin likita.
Falala ya ce bayan sun gama ganin likitan sai basu koma gida Katsina ba sai suka yada zango a gidan kanen sa dake Tudun Yola.
“Bayan sun isa cikin gidan sai Alkasin ya dauki sharbebiyar wuka ya caka wa mahaifin sa. Daga nana sai aka garzaya da shi asibiti inda a can ne ya rasu.
An yi jana’izan mahaifin Alkasim.
Bincike ya nuna cewa Alkasim dai ya samu tabuwar hankali ne dalilin shaye-shayen kwayoyi da ya ke yi.
Discussion about this post