Tawagar mawaƙin da aka yi garkuwa da shi da ‘yan amshi, ‘yan rawa, makaɗa da sanƙirar waɗanda ‘yan bindiga suka nausa da su cikin jeji a watan Disamba, sun samu kuɓuta, har sun yi bayanin yadda suka shafe kwanaki a hannun masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Cikin watan Disamba ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mawaƙi Omoba De Jombo da tawagar sa, a dajin Jihar Kogi.
A wata tattaunawa da BBC, mawaƙin da sauran ‘yan tawagar sa sun bayyana irin halin da suka tsinci kan su a hannun ‘yan bindiga.
Adebukoye Omooba ya ce an nausa da su daji a ranar 17 ga Disamba, kan hanyar su ta komawa gida daga bikin rufe gawa a garin Itaketo-Isao, Jihar Kogi.
Omooba ya ce da farko dai Naira miliyan 10 suka ce a biya kuɗin fansar duk mutum ɗaya.
Amma bayan mun riƙe su, sai suka rage farashi zuwa Naira miliyan 7 duk mutum ɗaya.
Ya ce masu garkuwar sun nemi ya nuna masu mutum uku da za su bindige idan aka yi lattin kai masu kuɗaɗen fansar.
“Na yi tunanin gara ya kashe ni kawai. Domin idan na nuna mutum uku sun bindige, to idan na koma gida da wane ido zan kalli iyalan su?
“Da na ce ba wanda zan iya nunawa, sai ya cika da mamaki sannan ya tafi.”
Ya ce kwanaki 6 da suka shafe a hannun ‘yan bindiga, tamkar shekara shida suka shafe a hannun su.
“Lokacin da aka haɗa kuɗaɗen fansar, an kasa samun zunzurutun kuɗi, saboda lokacin ana ta hada-hadar Kirsimeti, kuɗaɗe na wahala sosai.
“Sai dai aka roƙi shugaban ‘yan bindigar ya yi haƙuri ya karɓi dala, kuma da farko har ya amince, amma daga baya ya ce ba zai karɓi dala ba, sai Naira ya ke so kawai.”
Ya ce bayan kwanaki shida, sai aka sake su bayan an biya kuɗaɗen.
Ya ce daga yanzu sun daina zuwa gayyar kiɗa da waƙa a garin da babu filin saukar jirage.
Makaɗin garayar sa mai suna Tope Famakinwa, ya ce a kwanaki shida da suka shafe a hannun ‘yan bindiga, ba su cin komai sai ganyen bishiyoyi, saboda babu ruwa kuma babu abinci.
Makaɗin gangar su mai suna Sunday Olaleye, ya ce sai da ta kai sun riƙa shan fitsarin su domin kada ƙishirwa ta kashe su.
Sun ce an sake su bayan an kai wa ‘yan bindiga Naira miliyan 7 sau 13, wato Naira 101 kenan.
Discussion about this post