Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, ya bayyana cewa sai da ya shafe kwanaki bakwai bai rintsa ya yi barci ba, kafin a yanke hukuncin Kotun Ƙoli a shari’ar sa da ɗan takarar APC na Jihar, Air Mashal Abubakar.
Gwamna Bala ya faɗi haka a ranar Asabar, lokacin da yake wa magoya bayan sa jawabi a Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi, kwana ɗaya bayan nasarar da Kotun Ƙoli ta ba shi, a Abuja.
Duk da dai gwamnan bai bayyana sunayen waɗanda ya ke zargi ba, amma dai ya ce wasu shugabannin jihar na baya sun yi ta ƙirƙiro ƙarairayi da sharri a kan sa, domin a cire shi daga kan mulki ko ta halin ƙaƙa.
Daga nan ya ƙalubalanci waɗanda ya ce masu adawar da shi ne su nuna asalin su a Bauchi. Ya ƙara da cewa alfarma aka yi wa tsoffin gwamnonin jihar da suka riƙa ƙulla masa sharri, har suka samu ma suka yi gwamna, amma kuma su ne a yanzu ke masa tuggu da sharrin raba shi da kujerar sa.
Daga nan ya ƙara da cewa daga yanzu ba za sake bari baƙin ‘yan siyasar da jama’ar Jihar Bauchi ba su san su ba, su sake yin mulki a jihar.
“Wasu tsoffin gwamnonin jihar nan ne suka haddasa min rashin barci na tsawon kwanaki baki, saboda sun yi ta ƙirƙiro ƙarairayi da sharri da tuggu a kai na can a Fadar Shugaban Ƙasa, don kawai a ƙwace min nasarar da na samu ko ta halin ƙaƙa,” cewar Gwamna Bala.
“Sun yi iyakar ƙoƙarin ganin sun haɗa ni faɗa da aboki na, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, har ma da Shugaban Ƙasa ɗungurugum, Bola Ahmed Tinubu.
“Sun shaida wa Fadar Shugaban Ƙasa cewa wai ni ne matsala, kuma idan na ci gaba da zama kan mulki, zan ba su matsala,” haka Bala ya shaida wa cincirindon jama’a.
Ya ce to shi dai duk da ɗan jam’iyyar adawa ne, ya na da kyakkyawar alaƙa da Shugaba Tinubu.
Sannan ya ce ya yi sa’a Tinubu na son irin ayyukan alherin da ya ke yi a Jihar Bauchi.
Discussion about this post