Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) a ranar Alhamis sun kai samame hedikwatar rukunin kamfanonin Dangote dangane da binciken da ake yi kan kudaden musanyen Daloli da ake yi yanzu haka a kasar nan.
Majiyoyi sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa, a lokacin da jami’an EFCC suka isa hedikwatar kamfanin da ke Legas, sun bukaci wasu takardu da suka shafi rabon musayan kudaden kasashen waje da aka baiwa kamfanin a cikin shekaru goma da suka wuce.
Daga nan ne suka binciki takardun da jami’an kamfanin suka bayar na tsawon sa’o’i, inda suka kwashe wasu daga cikinsu suka yi awon gaba da su.
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa hukumar EFCC ta rubutawa wasu kamfanoni 52 wasika inda ta umurce su da su ba su takardun da ke nuna yanayin yadda aka rika basu musanyen kudaden waje a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Masu bincike a watannin da suka gabata sun zargi CBN da fifita wasu mutane da kamfanoni da kuma wadatar da su ta hanyar raba musu kudaden waje ba tare da an bi ka’ida ba.
Majiya ta shaida mana cewa duk da cewa wasu kamfanoni sun mika takardun su, wasu sun nemi a ba su lokaci domin su tattara su kawo wa EFFC takardun.
Sai dai kuma maimakon EFCC ta jira rukunin Dangote ta kai mata nata takardun, sai ta yi wa Kamfain diran mikiya don ta tozarta ta, duk da cewa Kamfanin ta shirya tsaf domin kai wa EFCC takardun kai tsaye.
” Irin wannan abi da aka yi wa Kamfani irin na Dangote, zai iya sa ma su son saka jari a Najeriya, su canja tunanin ganin cewa wannan Kamfani ba karamar Kamfani ba ne da za a yi mashi irin wannan kutse.
PREMIUM TIMES ta nemi ji daga bakin shugaban kakakin EFCC amma bai maida kirar waya da aka yi masa ba.
Discussion about this post