Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta umarci Gwamnan Kano, Abba Yusuf cewa ya biya Honarabul Ado Doguwa diyyar Naira miliyan 25, saboda ɓata masa suna a ƙarar zargin kisa da aka shigar kan ɗan majalisar.
Kotun ta kuma umarci Gwamnan ko gwamnatin sa kafa ta ƙara keta haƙƙin ɗan Adam da ‘yancin walwalar Doguwa.
Kamfanin Dillancin Labarai ya buga labarin cewa Doguwa, wanda ke wakiltar Ƙananan Hukumomin Tudun Wada da Doguwa a Jihar Kano, an kama shi ne a ranar 28 ga Fabrairu a filin jirgin Malam Aminu Kano, bisa zargin sa da laifin jan zugar ‘yan daba, suka banka wa sakateriyar NNPP wuta, a Tudun Wada, har aka rasa rayukan ‘yan NNPP biyu a gobarar.
Duk da ɗan majalisar ya musanta zargin da ake yi masa, an maka shi kotu a cikin watan Maris, a Kano, daga nan aka tsare shi a kurkuku.
Daga baya an bayar da belin sa kan Naira miliyan 500 a Babbar Kotun Tarayya, ta Kano.
Sai dai kuma mai gabatar da ƙara ya janye gurfanar da shi kotu, bayan ya ce ya kasa samun ƙwararan hujjojin da zai iya gurfanar da shi a gaban mai shari’a.
Sai dai kuma Doguwa, a ta hannun lauyan sa Afam Osigwe, ya shigar da ƙarar neman kare haƙƙin Doguwa, daga yunƙurin sake kama shi da Gwamnatin Kano ke neman yi, dangane da tashin hankali a lokacin zaɓen ɗan majalisar tarayya da na shugaban ƙasa.
Bayan doguwar kika-kaka, kotu ta hana sake kama Doguwa, kuma ta umarci gwamnatin Kano ta biya shi diyyar naira miliyan 25, saboda an tayar masa da hankali, kuma daga baya aka janye ƙara.
Discussion about this post