Akalla mutane 16 ne aka kashe a kauyen Mushu da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato.
Mai magana da yawun rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar, Oya James, ya tabbatar wa wakilinmu a Jos faruwar lamarin.
A cewar Kaftin James, an kai harin ne a daren ranar Asabar yayin da mazauna unguwar da aka kai wa harin ke barci.
Ya kara da cewa, “bayan harin an baza jami’an tsaro domin dakile tsahin hankali a yankin domin an dan samu barkewar tashin hankali bayan faruwar lamarin amma an shawo kan sa.
A halin da ake ciki, Gwamna Caleb Mutfwang ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa al’ummar, yana mai bayyana harin a matsayin dabbanci, rashin tausayi da bai kamata a ce an yi shi.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Gwamnan, Gyang Bere ya fitar, ta ce gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta kamo wadanda suka aikata wannan munanan tare da tabbatar da an hukunta su.
Discussion about this post