Basaraken Ife, Oonin na Ife Adeyeye Ogunwusi ya bayyana cewa kowace mace na da salon maita da take da shi a jikin ta.
Ogunwusi ya fadi haka ne da yake tattaunawa da gungun mata ƴan wasan kwaikwayo a lokacin da suka kawo masa ziyara har fadarsa.
Matan waɗanda jarumai ne na wasan kwaikwayo wani shiri da ake nuna wa a Talbijin mai suna ‘Real Housewives’ sun kawo masa ziyarar gaisuwa ne har fadar sa.
A bidiyo da ya karaɗe yanar gizo anga jarumai kamar su Iyabo Ojo, Chioma Ikokwu da Tania Omotayo tare da basaraken a fadar sarkin.
A lokacin da basaraken ya shigo cikin fadar kowace mace ta durkusa domin gaishe da sarki.
Basaraken ya ce nau’in maita da suke dashi mai kyau ne sai dai mutane da dama na yi wa abin kallon wani abu da ba shi da kyau.
“Ita fa Mace tun daga halittar ta ta ke da nau’i na maita, sai dai kuma yadda kowacce ke amfani da na ta maitan ne ya banbanta.
Basarake Oni ya hore mata cewa maimakon su rika yin mugunta da baiwar maita da take da shi su rike yin abinda ya dace da shi na alkhairi.
Ɗaya daga cikin jaruman Iyabo ta ne mi Sarki Ooni ya yi mata karin haske game da wannan maita da yake ikirarin duk mata na dashi, sai ya bata amsar cewa ” Ƙwarai duk mata na da maita, sai dai ya hore su da su rika yin abu mai kyau da shi.
Discussion about this post