Da dukkanin alamu, Hadakkar Fansho ta Kananan Hukumomi da Jaha a Jigawa, ta fara shiga garari, matsalar na neman azzara mutuka.
Cin bashi domin biyan giratuti fa, tamkar cin bashin tallaka ne, an ci don abiya bukata, a kwai Jan aiki, a ce an samu wadatar da za a biya kuma a samu doriya ta ci gaba.
Jagorancin wannan hukuma fa yana kokarin kafa tarihi, tunda a ka kafashi don kawo karshen matsalar Fansho a baya, a yanzu yana kokarin gaza yin aikinsa, ma’aikatan da suka yi ritaya na kokarin shafe shekara ba tare da an biya su hakkokin su ba.
Hukumar Hadakkar Fansho na Jihar Jigawa,wadda a ka kafata a mulkin tsoho Gwamna Alhaji Saminu Turaki.
Dokar Fanshon, sashe na hudu Jigawa State (Local Government and State) Contributory Pension Scheme, ya ce ya zama dole kowane ma’aikaci ya bayar da Kashi Takwas na kashin albashin sa, sannan Kananan Hukumomin da Jaha ta bada Kashi goma sha bakwai na kashin albashin ma’aikatan ga wannan asusu, domin biyan hakokin ma’aikatan yayi da suka bar aiki da cigaba da biyan su Fansho na wata wata.
Kusan wannan shine tsawan lokacin da a ka dauka a tarihin kafa wannan hukuma ta Fansho da ma’aikata suka yi ritaya, har wasu sun shiga hali na damuwa da matsanancin talauchi, dalilin rashin biyan su hakin su.
Kusan a tsawan lokaci, masana da masu sharhi sun sha jan hankalin mahukunta a kan aukuwar wannan matsalar.
A ranar 17 ga watan Augusta ma, Jaridar Premium Times ta bada wani ruhoto na bincike a hukumar Fanshon Jigawa ta nuna yadda Kananan Hukumomin jahar a mulkin baya suka share kusan shekara biyar ba tare da sanya kason su ba a hukumar Hadakkar Fanshon.
Duk da cewa Gwamnati ta kafa kwamati don binciken al’amuran wannan hukuma, amma babu wani takamaiman bayani a kan wannan batu, amma a dukkanin alamu dai akwai ruwa a kaba.
A yanzu mutane, musamman ma’aikata wanda wannan matsala tafi shafa kai tsaye, zasu yarda da tsinkayar da akayi tayi a kan wannan batu, tunda a yau an kai ga nemo aron bashin kudi don biyan ma’aikatan da suka yi ritaya.
Sanarwa bayan taron Majalissar Zartarwa ta Jihar Jigawa, na cewar za a rantawa Hukumar Fanshon Jigawa zunzuruntun kudi har Naita Biliyan Biyu, domin biyan ma’aikatan da suka yi ritaya a wannan shekarar mai karewa.
Wannan ba karamin batu bane wanda duk masu ruwa da tsaki da su sake lura da yadda wañan tsari yake tafiya.
In a yanzu aka ce, sai anci bashi don biyan hakkin ma’aikata, to yaya zai kasance ga ma’aikata masu ritaya a nan gaba.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post