Hausawa na cewa ‘Sarki goma zamani goma’. Irin yadda aka riƙa zargin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya riƙa naɗa masu kashi a gindi a gwamnatin sa, haka abin ya ke yanzu haka a ƙarƙashin mulkin Tinubu.
Daga cikin abin da aka zargin Buhari da yin babban kuskure da sakaci, shi ne yadda ya ƙi cire Godwin Emefiele daga matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, duk da zarge-zargen da aka yi masa wajen laifin haddasa karyewar darajar Naira tun a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.
Maimakon Buhari ya canja Emefiele, sai ya bar shi har ya yi shekaru takwas na wa’adin sa ya na tare da Emefiele.
A yanzu kowa ya ga irin ƙadabolon da ake yi kan Emefiele, wanda ake zargi da ɓoye biliyoyin kuɗaɗen Najeriya a bankuna ƙasashen waje dama da 590.
Tinubu ya bai wa ‘yan Najeriya mamaki, ganin yadda ya naɗa tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle muƙamin Ƙaramin Ministan Tsaro.
An naɗa shi ne a daidai lokacin da ya ke kan siraɗin zargin da EFCC ke yi masa na karkatar Naira biliyan 70.
Maimakon a ji labarin EFCC ta kama damƙe Matawalle, sai Tinubu ya naɗa shi Ƙaramin Ministan Tsaro, shi kuma tsohon Shugaban EFCC, Bawa, aka kama shi aka tsare, ya shafe watanni tsare a hannun SSS.
Naɗa tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Bagudu Ministan Kasafin Kuɗaɗe da Tsare-tsare ya bai wa jama’a da dama mamaki. Bagudu wanda binciken ƙaƙudubar satar kuɗaɗen Najeriya a zamanin gwamnatin marigayi Sani Abacha, ya fallasa cewa Bagudu ne babban ɗan kamashon lodi, jigila da saukalen miliyoyin dalolin Najeriya zuwa ƙasashen Turai.
An yi tunanin cewa Tinubu zai yi kaffa-kaffa da Bagudu, sai ma ya rungumo shi ya ba shi muƙamin Ministan Kasafin Kuɗaɗe.
Naɗa tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje shugabancin APC ma ya nuna wa ‘yan Najeriya cewa batun yaƙi da rashawa da Tinubu ya ce zai yi, to ya zama tatsuniya kawai.
An yi ta zumuɗin Ganduje ya sauka daga mulki domin a gurfanar da shi dangane da zargin karɓar rashawa ta miliyan dalolin da aka nuno shi ya na karɓa a bidiyo, an naɗa shi shugabancin APC, jam’iyya mai mulki.
Haka nan naɗa Godswill Akpabio matsayin Shugaban Majalisar Dattawa, ya bai wa ɗimbin jama’a mamaki. Tun bayan zargin satar biliyan 103 da aka yi masa lokacin da ya sauka daga Gwamnan Jihar Akwa Ibom, a 2023, maganar ta mutu murus, bayan da Akpabio ya koma APC, har tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya naɗa shi Shugaban Hukumar Raya Yankunan Yankin Neja Delta.
Discussion about this post