Ƙungiyar Sa-ido Kan Zaɓuɓɓuka ta Yiaga Africa, ta bankaɗo kwafen takardun da ke ɗauke da sakamakon zaɓe, tun kafin a jefa ƙuri’a.
Lamarin ya faru a safiyar Asabar, a Jihar Kogi, inda tuni ƙungiyar ta ankarar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC cewa ta gaggauta yin bincike, tare da yi wa duniya bayani gamsasshe.
Yiaga ta buga hoton kwafen takardar ta INEC mai ɗauke da sakamakon zaɓen, a lokacin da ko zaɓen ba a ma fara ba.
Ta buga takardar a shafin ta na Tiwita, ƙarfe 9:20 na safiya, kuma ta yi wa INEC kiran gaggawar cewa ta yi sauri ta binciki wannan matsala.
Takardar da Yiaga ta buga na ɗauke da sakamakon zaɓen Rumfar Zaɓe ta PU 004 ta Mazaɓar Eni cikin yankin Ogiri/Magojo.
Tuni dai aka fara fafata kokawar hawa kujerar wanda zai gaji Gwamna Yahaya Bello.
Akwai rumfar zaɓe 3,541 a Jihar Kogi, inda ‘yan takara 5 ne a sahun gaban sauran ‘yan takara 15 da ke bayan su.
Mutum 1,833,160 suka karɓi katin shaidar rajistar zaɓe a Kogi, inda za a yi zaɓe tsakanin ‘yan takara.
Akwai ƙananan hukumoni 21 a Kogi. Dino Melaye na PDP zai so ya yi nasara kan Ahmad Ododo na APC, kamar yadda shi ma Ododo ɗin zai so yin nasara kan Dino na PDP, Murtala Ajaka na SDP, Leke Abajide na AC da Olayinka Braimoh na AA.
Ana fargabar kada a sake maimaita irin balahirar tashin hankalin da aka yi a zaɓen 2019.
Gwamna Yahaya Bello wanda tun ƙarfe 9:18 na safiya ya isa rumfar zaɓe domin jefa ƙuri’a, zai kammala wa’adin sa ne a ranar 27 ga Janairu, 2024.
Discussion about this post